’Yan sanda a Jihar Kano sun cafke wani mutum da ya kware wajen buga takardun daukar aiki ta jabu.
Mutumin mai shekara 61 mazaunin Karamar Hukumar Dala a Kano ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi bayan da ’yan sanda suka titsiye shi.
- An kama magidancin da ya yi garkuwa da kansa a Kano
- An cafke matar da ta kashe ’ya’yanta 2 a Kano
- An kashe matashi kan budurwa a Kano
- #EndSARS: Kwamandan ’yan sanda ya tsallake rijiya da baya
Ya bayyana wa jami’an tsaro cewa shi da wasu mutane uku ne suke gudanar da sana’ar sayar da takardar daukar aiki na bogi.
Ya kara da cewa suna sayar da takardar daukar aikin akan kudi da ya kama daga Naira dubu arba’in zuwa dubu sittin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun cafke mutumin ne bayan koken da wata mata ta shigar cewa wanda ake zargin sun damfare ta.
Ye ce an kama wanda ake zargin tare da wasu takardun daukar aiki na jabu da kuma kudi kusan Naira miliyan hudu.
Daga karshe kakakin rundunar ya gargadi jama’a da su kula domin kauce wa fadawa hannun bata-gari da sunan neman aiki.