✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun direban da ke kai wa ’yan bindiga fasinjoji a Kano ta cika

Direban ya ce ya kan tura wa masu garkuwa da mutane sako da zarar ya dauki fasinja.

Wani direban mota da ya kware wajen dibar fasinjoji a motarsa sannan ya mika su zuwa ga masu garkuwa a Kano ya shiga hannun hukuma.

Wanda ake zargin ya shiga hannun jami’an ’yan sandan da ke yaki da masu garkuwa da mutane.

Direban, mai kimanin shekara 25 a duniya, na daga cikin gawurtattun mutane da jami’an tsaro suka cafke a Abuja.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, CP Frank Mba ne ya bayyana hakan, inda ya ce an yi nasarar cafke shi ne bayan samun bayanan sirri kan yadda yake yaudarar mutane zuwa ga ’yan bindigar.

Rahotanni sun bayyana yadda direban ke yaudarar mutane da ke zaune a yankin Janguza da Rijiyar Zaki zuwa Jami’ar Bayero ta Kano da ke da dubban dalibai a yankin.

Kazalika, bincike ya nuna yadda mutumin ke yin basaja a matsayin direba ko fasinja, daga nan ya yaudari mutane ya mika su ga ’yan bindiga.

Yayin da yake amsa tambayoyi a hannun jami’an ’yan sanda, wanda ake zargin ya ce, “Idan na dauki fasinja na kan tura wa masu garkuwar sako, wanda daga nan za su tare motar a wani wajen sai su sace su,” a cewarsa.