Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da satar sassan jirgin kasa a Zariya, jihar Kaduna.
Ofishin hukumar dake kula da Arewacin Najeriya dake garin na Zariya ne ya tabbatar da kamun mutanen a ranar Juma’a.
- An kashe kaji 27,000 a Bauchi saboda takaita yaduwar Murar Tsuntsaye
- An tsinci gawar dalibi a Kano bayan kwana 5 da batansa
Ayyukan barayin dai a ’yan kwanakin nan ya jima yana gurgunta harkar sufurin jiragen kasa.
Ko a makon da ya gabata sai da wani jirgin da ya taso daga jihar Legas da nufin zuwa Zariya makare da fayif-fayif na ruwa ya ci karo da makamantan wadannan barayin a Unguwar Kanawa dake Kaduna.
Yayin da yake gabatar da ayarin barayin a Zariya, Injiniyan dake kula da shiyyar Arewa na hukumar, Haruna Sabo ya ce dubun barayin ta cika ne bayan wani ma’aikacin hukumar ya kama su a gundumar Sayi-Dumbi dake hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Juma’a.
Haruna ya ce dama hukumar ta girke wasu jami’anta domin su ci gaba da yin sintiri a kan titunan jiragen a kullum, yana mai cewa sun dauki matakin ne da nufin kakkabe bata-garin.
“Wadannan jami’an na tsaka da aiki ne sai suka ci karo da wadannan bata-garin suna kwance notuka da karafan da ke rike da jirgin,” inji shi.
Injiniyan ya kuma lura cewa kwance irin wadannan karafa da notukan sune ummul-aba’isun tangardar jiragen, wanda ya ce zai kuma iya haddasa mummunan hatsari.
Ya ce tuni binciken ’yan sanda ya taimaka musu wajen gano masu sayen irin wadannan kayayyakin kuma za a mika su ofishin ’yan sanda na hukumar dake Zariya domin fadada bincike da kuma gano sauran masu hannu a ciki.