✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Dubun barayin mota ta cika a Kano

Dubun barayin ta cika bayan da ’yan sanda suka damke su.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wasu kasurguman barayi da suka sace wata mota kirar Toyota Hilux da wasu ababen hawa.

Wanda ake zargin ya fito daga Karamar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, kuma tawagar Puff Adder ta rundunar ’yan sandan karkashin jagorancin SP Rabi’u Ahmed, ne suka cafke a kan titin Jami’ar BUK a Kano.

Kakakin ’yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana gudanar da bincike kan wanda ake zargin, kuma an kama wanda ke taimaka masa, wanda ya kware wajen kera manyan makullai da kuma sayar da su ga barayi, kuma an kwato makullai 29 a hannunsa.

“A yayin binciken wanda ake zargin ya amsa laifin satar mota kirar Toyota Hilux a titin Madobi, Karamar Hukumar Kumbotso da ke Jihar Kano.

“Wanda ake zargin na cikin wata fitacciyar kungiyar da ta kware wajen satar mota daga inda aka ajiye su; A baya an kama shi da irin wannan laifin kuma an gurfanar da shi a gaban kotu,” inji Kiyawa.

Ya ce rundunar ta yi nasarar kama wasu barayin ababen hawa, da lambobin ababen hawan mutane a wajensu.

“Duk wanda aka sace motarsa ​​ya gano lambar motarsa ya kai rahoto a Sashen Hulda da Jama’a da ke Hedikwatar ’Yan Sanda a Bompai a Kano.”

A cewar Kiyawa, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na tsanaki sannan a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu.