✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dubban mutane sun canza sheka zuwa APC a Kebbi

Tsohon Ministan cikin gida da kuma wasanni da matasa, Alhaji Sa’idu Balarabe Sambawa ya bayyana cewa babu sauran mutumin kirki guda daya tak da ya…

Tsohon Ministan cikin gida da kuma wasanni da matasa, Alhaji Sa’idu Balarabe Sambawa ya bayyana cewa babu sauran mutumin kirki guda daya tak da ya ragu a cikin Jamiiyyar PDP a Jihar Kebbi. Sambawa, ya yi wannan furuci ne a gaban dimbin jama’ar da suka taru a filin wasa na tunawa da Sarkin Halliru Abdu dake Birnin Kebbi, domin bayyana aniyarsu ta canza sheka daga PDP zuwa APC.

Tsohon ministan ya ce a madadin Sanata Na’Amo Abdullahi da dukkanin magoya bayansu mutum dubu 140 wadanda suka fito daga kananan hukumomi 21sun yanke shawarar barin PDP zuwa APC domin irin akidar da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake da ita, da kuma irin ayyukan ci gaba da Gwamnan Jihar Kebbi ke yi a duk fadin Jihar Kebbi.     

Ya kuma kara da cewa kowa yasan irin muhimmiyar rawar da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yake takawa tun lokacin da ya rike shugabancin kasar nan musamman fannin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da kuma daidaita al’amurra a cikin ma’aikatun gwamnati da samar wa matasa aikin yi da kuma aiwatar da manyan ayyuka ga al’ummar kasa da kuma farfado da ayyukan gona.

Da yake tsokaci akan ayyukan da Gwamnan Jihar Kebbi ya yi, Sambawa ya ce, abin da ya kara masu kwarin gwiwar komawa APC shi ne irin cigaban da Jihar Kebbi ta samu, musamman ta fannin noman rani da damina da kuma manyan ayyukan da ake gudanar wa al’ummar Jihar Kebbi musamman samun wutar lantarki awa 24 ba tare da dauke ta ba sai da dalili, da kuma gina sabbin hanyoyi a dukkan kananan hukumomin jihar 21 da inganta harkar Ilimi, lafiya da kuma walwalar jama’a da biyan ma’aikata albashi akan kari da kuma biyan yan fansho kudadensu da makamantan su.

Da yake jawabi a wajen karbar wadanda suka canza shekar, shugaban APC na Jihar Kebbi, Attahiru Maccido, ya ce ya rasa abinda zai ce saboda kuwa gaskiya ta yi halinta, ada masu cewa Atiku Bagudu ba na kwarai ba ne mugu ne, to yau sun gane gaskiya daya ce karya hure take ba ta ya’ya’ inji shi. Sannan ya ce a yau duk sun zama daya babu bambanci.