Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yana daga cikin dubban Musulmin da suka halarci jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci nan da ke Kano Sheikh Aliyu Harazimi a kofar Fadar Sarkin Kano a shekaranjiya Laraba.
Fitaccen Shehin darikar Tijjaniyya Sheikh Aliyu Harazimi ya rasu yana da shekara 93 bayan gajeriyar rashin lafiya a gidansa da ke unguwar Hausawan Mandawari da ke karamar Hukumar Gwale da ke Jihar Kano
Khalifa Fatihu Ngibirima ne ya jagorancin Sallar jana’izar da misalin karfe 2:00 na rana, inda aka zarce da gawarsa zuwa gidansa aka binne shi.
Marigayi Sheikh Harazimi wanda daya ne daga cikin fitattun malaman darikar Tijjaniyya a Afirka ta Yamma ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya da kuma jikoki da dama kamar yadda majiyar iyalansa ta ce.
Sheikh Aliyu Harazimi bin Sani Muhammad ya rasu ne a cikin dare a gidansa a ranar Talatar da ta gabata.
Dubban Musulmi suka halarci jana’izar Sheikh Aliyu Harazimi
Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso yana daga cikin dubban Musulmin da suka halarci jana’izar fitaccen malamin addinin Musulunci nan da ke Kano Sheikh…
