Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta sake haramta wa ’yan Najeriya ziyartar kasarta ba tare da bayyana dalilinta na daukar wannan tsauttsauran mataki ba.
Kasar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta rarraba wa abokan huldar kasuwancinta daga Najeriya da suka hada da ejan-ejan da ke samar wa ’yan kasar takardun biza, matakin da ake ganin zai dada dagula rikicin diflomasiya tsakanin kasashen biyu.
Wannan na zuwa ne bayan ’yan makonni da Hadaddiyar Daular Larabawa ta tsaurara matakan bayar da biza ga sabbin bakin da ke marmarin shiga cikin kasar.
Sanarwar ta ce, hukumomin kasar sun soke daukacin bukatun neman takardun biza daga ’yan Najeriya da wasu kasashen Afirka na bakaken fata.
Kazalika mahukuntan na UAE sun ce, ba za su mayar wa ‘yan Najeriya kudaden da suka kashe ba wajen neman takardun bisar da suka soke, yayin da kawo yanzu suka ki bayar da dalilinsu na daukar matakin.
Ba a karon farko kenan ba da Hadaddiyar Daular Larabawa ke sanya jerin takunkumai kan ’yan Najeriya, al’amarin da ya dada cakuda huldar diflomasiyar da ke tsakaninsu.
’Yan Najeriya da dama da suka hada da ’yan kasuwa da ’yan siyasa da ma’aikatan gwamnati na yawan ziyartar Dubai domin shakatawa ko kuma harkar kasuwanci da dai sauransu.