An yanke wa ’yan Najeriya shida hukunci a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) bisa zargin daukar nauyin ayyukan kungiyar Boko Haram.
Wata kotu dai a kasar ta yanke wa biyu daga cikinsu, Surajo Abubakar Muhammad da Saleh Yusuf Adamu hukuncin daurin rai-da-rai, sai Ibrahim Ali Alhassan, AbdurRahman Ado Musa, Bashir Ali Yusuf da Muhammad Ibrahim Isa, wadanda aka yanke wa kowannensu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.
- Za a iya magance rikicin Boko Haram a siyasance – Zulum
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 75
- Yadda na kubuta daga hannun Boko Haram – ’Yar shekara 13
- Sojoji sun bindige ’yan Boko Haram 22 a Borno
Kotun ta bayyana cewa an kama su ne bisa zargin aikata laifin aika wa da ’yan kungiyar Boko Haram kudi Dala dubu 782 daga tsakanin shekara ta 2015 zuwa 2016.
Wakilinmu ya rawaito cewa sama da shekaru 11 ke nan da ta’addacin Boko Haram ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
‘Sharri aka yi musu’
Sai dai iyalan wadanda ake zargin sun musanta, inda suka shaida wa Aminiya cewa tun kafin a kama su, suna gudanar da kasuwancin canjin kudi a Dubai din.
Sai dai an gabatar wa da kotu hujojjin da suka nuna sun tura wa ’yan Boko Haram kudi daga Dubai zuwa Najeriya, wanda hakan ya saba da dokar Hadaddiyar Daular Larabawan karkashin sashi na uku da na 29 na shekarar 2017.
Yadda aka kama su
Kotu ta aike da takardar izinin kama masu laifin ga hukumar kula da harkar canjin kudi ta kasar, bayan da bincike ya gabata cewar suna da alaka da ’yan kungiyar.
An kama masu laifin ne a gidajensu ranar 16 da 17 ga watan Afrilun shekarar 2017 bayan an binciki gidanjen nasu domin samun wasu bayanai.
Mutum na farko da na biyu kuwa an same su da laifin shiga kungiyar Boko Haram, wanda ya saba da dokar ta’addancin kasar karkashin sashe na 22 (2) na shekarar 2017, wanda aka tanadar musu shukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma daurin rai-da-rai a gidan kaso.
Ragowar hudun kuma an same su da laifin taimaka wa ayyukan ‘yan Boko Haram, wanda hukuncinsu shi ne daurin rai da rai ko daurin shekaru biyar zuwa sama a gidan yari, kamar yadda dokar hadaddiyar daular Larabawan ta tanadar.
Yadda lamarin ya faru
Lamarin dai ya samo asali ne bayan tura kudi ga wani mutum mai suna Alhaji Sa’idu, wanda mazaunin Najeriya ne, kuma bincike ya tabbatar da cewa shi ne yake gudanar wa Boko Haram wasu harkoki da suka shafi kudade.
Sai kuma Alhaji Ashiru wanda shi ma bincike ya tabbatar da cewa babban jami’in gwamnati ne yana da hannu wajen taimaka musu wajen daukar dawainiyar da ta shafi kudi.
To sai dai, iyalan wadanda ake zargin sun shaida wa wakilinmu cewa yaudarar su aka yi da sunan harkar kasuwancin canji aka cimma wata bukata ta Boko Haram ba da saninsu ba.
‘Ba a musu adalci ba’
Auwalu Ali Alhassan wanda dan uwa ne ga Ibrahim Ali da Bashir Ali, ya bayyana cewa ba a yi musu adalci yayin zartar da hukuncin ba domin ba a ba su damar gabatar da shaidu ba.
Ya kuma ce sun kasa samun nasarar zama da masu ruwa da tsaki na gwamnatin Najeriya dangane da lamarin.
“Ba a musu adalci ba lokacin yanke hukuncin. Da farko an kama su da laifin buga jabun kudi yanzu kuma al’amarin ya sauya zuwa ta’addanci”, a cewar Alhassan.
Ya kara da cewa sun kai maganar gaban Ma’aikatar Kula da Harkokin Kasashen Waje wacce ta ce su jira zuwa lokacin da za a ba su damar daukaka kara.
Alhassan ya kara da cewa a wannan lokacin sai da ya gana da Minista a Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Khadija Bukar Abba Ibrahim, da kuma jakadan UAE a Najeriya a kan lamarin inda suka ba shi tabbacin za a saki masu laifin tare da dawo da su gida.
Yadda suka koma Dubai
Alhassan ya bayyana cewa ’yan uwansa sun koma Dubai domin ci gaba da harkar canji ne saboda yadda kasuwancin ya fi tafiya a can, wanda shi ne dalilin da ya sa suka yanke hukuncin tura Ibrahim.
Ya kara da cewa Ibrahim yana huldar kasuwanci da mutane daban-daban har da wasu a kasashe kamar China da Dubai.
Abin da hukumar Shari’a ta ce
Da aka tuntubi Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce gwamnatin Najeriya na sane da faruwar lamarin, kuma tuni ta aike wa gwamnatin Dubai takardar bukatar rahoton binciken kan wadanda ake zargin wanda har yanzu a cewarsa ba a damka wa gwamnatin Najeriya ba.
Ya kuma musanta batun da iyalan masu laifin suka yi na cewa gwamanatin ba ta yi komai kan lamarin ba.
Malami ya ce, “Gwamnatin Najeriya ta aika a rubuce cewa tana bukatar rahoton binciken da mahukuntan Dubai suka yi wanda har yanzu basu turo mana ba.
“Wannan al’amari ne da ya shafi UAE, dole sai dai mun bi a hankali domin shawo kan lamarin”, cewar Malami.
Ra’ayin lauyoyi
Barista Yusuf Mohammed Ahmed wani kwararren lauya a Kano ya bayyana cewa sai dai su daukaka kara zuwa Kotun Koli in har kasar ta Dubai na da ita, wanda a can ne kadai za su iya kalubalantar hukuncin da aka yanke musu.
“A lokuta da dama kotuna kan yanke hukunci iri daya ne, amma Kotun Koli ita kadai ce za ta iya sake hukunci ko kuma shari’ar baki daya,” a cewar Yusuf.
Shi kuwa Barista Ahmed Sani wani lauya ne a Abuja, cewa ya yi za a iya warware wannan hukunci ta hanyar alakar kasa da kasa, in har aka gano cewa ba su da hannu kai tsaye wajen hulda da kungiyar ta Boko Haram.
“Na ga akwai alamun rashin gogewa a tare da wanda aka yanke wa hukuncin, saboda kasashen Larabawa ba sa daukar abu da wasa musamman idan ya hada harkar ta’addanci, amma za a iya warware komai ta hanyar alakar kasa da kasa,” inji Sani.