Jagoran haramtacciyar Kungiyar nan ta ’yan awaren Biyafara, Nnamdi Kanu zai ci gaba da zama a tsare har zuwa ranar 21 ga watan Oktoban 2021 mai zuwa.
Hakan dai na zuwa ne bayan Gwamnatin Tarayya ta gaza gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda a nan ne ya kamata a gurfanar da shi a ranar Litinin.
- Masu garkuwa sun koma karbar kudin fansa ta banki a Abuja
- Buhari zai shafe mako biyu a Landan —Fadar Shugaban Kasa
Alkalin kotun, Mai Shari’a Binta Murtala Nyako ce ta bayar da umarnin dage zaman kotun da kuma ci gaba da tsare Kanu a hannun Hukumar Tsaro ta DSS har zuwa lokacin.
Kanu, wanda tun bayan kamun da aka yi masa tare da dawo da shi Najeriya yake hannun DSS, ya roki kotun da ta mayar da shi Gidan Yarin Kuje a daga hannun DSS din.
Bayan dawo da shi Najeriya, Mai Shari’a Binta Murtala Nyako wacce a baya ta bayar da shi beli bisa dalilai na rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a hannun DSS har zuwa 26 ga watan Yuli, 2021.