Rahotanni na bayyana cewa hukumar tsaro ta DSS ta cafke Sunusi Oscar 44 na masana’antar Kannywood, bisa furta kalaman barazanar kisa.
Wata majiya a Gwamnatin Kano da ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa an kama Oscar ne ranar Lahadi, saboda wani sakon murya na da ake zargin ya aika wa guda daga cikin jiga-jigan Gwamnatin Kano, inda yake barazanar halaka shi.
Da fari dai an fara alakanta kama 442 ne da Shugaban Hukumar Tace Finafinai na Kano Abba Almustapha, sakamakon rashin jituwar da ke tsakaninsu, tun bayan darewar sabuwar Gwamnatin Kano ta NNPP kan karagar mulki.
Rashin jituwar tasu dai ya samo asli ne saboda kalaman suka da Sunusi Oscar ya yi kan Almustaphan, inda yake cewa yana jawo ’yan adawa a jika, bayan a baya muzguna musu suka yi lokacin da ludayinsu ke kan dawo.
- Akwai buƙatar gwamnatin Najeriya ta cire tallafin wutar lantarki — IMF
- Ba mu da hannu a kara farashin kayan abinci – ’Yan kasuwar Singa
Wadannan kalamai dai sun janyo ce-ce-ku-ce a Kannywood, inda wasu ke goyon Oscar, wasu kuma ke ganin ko kadan ba su dace ba, domin lokaci ya yi da ya kamata su hada kawunansu su ajiye batun siyasa.
Sai dai wutar rigimar ta ci gaba da ruruwa, duk da cewa Oscar ya samu mukamin hadimin Gwamnan Kano, inda ya dinga kaurace wa tarukan hukumar ta tace fina-finan, da kuma sukar shugabancin Abba Almustaphan.
Majiyar ta mu dai ta bayyana cewa za a ci gaba da tsare Oscar ne, har zuwa lokacin da DSS za ta kammala bincike.