✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta tsare mahaifin matar Tukur Mamu

DSS ta sako matan Tukur Mamu amma ta ci gaba da tsare shi da dan uwan matarsa.

Hukumar Tsaro ta DSS ta Abdullahi Mashi, mahaifin matar Tukur Mamu, wanda ya yi fice wajen shiga tsakani wajen tattauanawa da ’yan bindiga domin sako fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna.

Bayan tsare Abdullahi Mashi, jami’an DSS sun kuma mai samame gidan dan uwan matar Tukur Mamu, Ibrahim Tinja, wanda ake tsare tare da dawo da su daga Najeriya tare da Tukur Mamu da iyalansa.

A ranar Laraba ne Aminiya ta kawo rahoton yadda DSS ta tsare mamu wanda dan jarida ne kuma shugaban kamfanin jarida na Fuza Communications, masu wallafa jaridar Desert Hereld.

Sai dai hukumar ta saki matan dan jaridar, amma ta ci gaba da tsare shi tare da dan uwan matarsa.

DSS ta yi awon gaba da shi ne a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, bayan jami’an tsaro sun tsare shi a kasar Masar.

Kafin dawo da shi Najeriya, Mamu ya shaida wa Aminiya cewa jami’an tsaron Masar sun tsare shi da iyalansa ne a filin jirgi na Alkahira, a hanyarsa da iyalansa ta zuwa Umrah.

Ya bayyana cewa an tsare shi ne bisa umarnin gwamantin Najeriya.