Hukumar tsaro ta DSS ta ce tana tsare da matashin malamain nan da ake zargi da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Kano, mai suna Baffa Hotoro.
Hakan na zuwa ne bayan a watan da ya gabata Ma’aikatar Harkokin Addinai na Jihar Kano ta sanar cewa DSS ta tsare Baffa Hotoro da abokinsa, Habib Haroun (Abu Aaman), bisa zargin munana lafazi ga Annabi Muhammad (SAW).
- Muna binciken gwamnan Zamfara kan N70bn —EFCC
- An kama ’yan Najeriya kan safarar hodar Iblis a Saudiyya
Bayan sanarwar matashin ya fito a wani bidiyo ya karyata kama shi, inda ya ce yana Umara a lokacin; Amma a ranar Alhamis hukumar ta ce matashin yana hannunta.
A baya dai, Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano, Ustaz Muhammad Nazifi Bichi, ya shaida wa Aminiya cewa sun karbi korafe-korafen zargin batanci a kan matasan malaman, wanda hakan ya sa hukumar ta sanar da DSS don daukar matakin da ya dace.
A cewar Daraktan, sun lura cewa rayuwar malaman ma tana cikin hatsari don haka ya zama dole su shiga cikin lamarin.
Baffa Hotoro ya ce kalaman malamin suna kan daidai, har ma ya kara da nasa, lamarin da ya janyo al’ummar jihar suka rubuta takardun korafi a kansa tare da neman hukumomi su shiga cikin lamarin.