Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta saki tsohon Mai Taimakawa Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan harkokin watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai.
Mahaifinsa, Alhaji Tanko Yakasai ne ya tabbatar da hakan a daren ranar Litinin.
Idan dai za a iya tunawa, DSS ta cafke Salihu ne ranar Juma’a bayan ya caccaki salon yadda jam’iyyarsu ta APC take tafiyar da harkokin tsaron kasa a shafinsa na Twitter, inda ya ce ta gaza a dukkan matakai kuma ya kamata ya sauka daga mulki.
Sa’o’i kadan da wallafa hakan jami’an DSS suka cika hannu da shi sannan kuma Gwamna Ganduje ya sallame shi daga kan mukamaminsa.
Gwamnan dai ya ce ya dakatar da shi ne saboda ba ya yi wa bakinsa linzami, lamarin da ya saba da tsarin jam’iyyarsu ta APC wacce yake hidimta wa.
Sai dai mahaifin Salihun, Alhaji Tanko Yakasai ya ce dan nasa bai karya kowace irin doka ba, hasali ma gaskiya ya fada cewa APC ta gaza.
Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar su dauki matakin shari’a a kan kamen, Yakasai ya ce tattaunawar tasu da DSS ce kawai za ta tabbatar da haka.