✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta kama Tukur Mamu a filin jirgin sama a Kano

Jami’an Hukumar Tsaro na Farin Kaya (DSS) sun dauko Malam Tukur Mamu a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Jami’an Hukumar Tsaro na Farin Kaya (DSS) sun dauko Malam Tukur Mamu a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Aminiya ta ruwaito yadda aka kama Mamu a Alkahira, babban birnin Kasar Masar, aka dawo da shi Najeriya.

Tsohon mai sasantawa tsakanin ’yan bindiga da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna ya ce shi da iyalansa sun nufi kasar Saudiyya domin aikin Umrah ne a lokacin da aka kama su aka tsare shi a kasar Masar na tsawon sa’a 24.

Aminiya ta gano cewa, yayin da jirgin Egypt Air da suke ciki ya isa Kano da misalin karfe 1:55 na ranar Laraba; Jami’an DSS sun tare kofar shiga filin jirgin mintuna kadan kafin jirgin ya sauka.

An dai lura da cewa, jami’an tsaro dauke da muggan makamai ciki har da sanye da fararen kaya, suna gadi a kofar shiga bangaren masu sauka daga jirgi, yayin da suka ajiye wasu motoci uku dauke a kofar shiga.

Ba a jima ba fasinjoji suka fara fitowa daga sashin isowa ba, daya daga cikin motar hilux din ta matsa gaba yayin da jakunkuna da ake tunanin na Mamu da iyalansa ne, aka loda su a daya daga cikin motocin guda biyu.

Daga baya motocin biyu sun yi gaba sannan wata bus ta shiga tsakanin su kafin daga bisani suka wuce tare.

Bayan tsare Mamu da iyalansa, sun shiga cikin motar bus din bayan an kama su a kofar shiga ta fasinjojin jirgin.

Wani dan uwa ga Mamu ya tabbatar da cewa, an kama Mamu da iyalansa kuma an kai su Abuja.

Wata majiya a ofishin DSS a Abuja ta kuma tabbatar da cewa an kama Mamu.

Daga: Jamilu Adamu da Clement A. Oloyede da Idowu Isamotu