✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta kama mutumin da ya yi garkuwa da mahaifiyar Rarara

Jami’an na DSS sun ƙwato Naira miliyan 26.5 a yayin wannan aiki da suka gudanar.

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta cafke daya daga cikin waɗanda suka kitsa sace mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.

Aminiya ta ruwaito cewa jami’an tsaron sun samu nasarar kashe ɗaya daga cikin ababen zargin da kuma ƙwato Naira miliyan 26.5 a yayin wannan aiki da suka gudanar.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa bayan samun bayanan sirri ne wasu jami’an hukumar ta DSS a reshenta da ke Kano suka ka yi dirar mikiya kan gungun masu garkuwar su biyar a wani daji da ke Makarfi sun tsakar rabon kudin fansar da suka karɓa.

Ɗaga daga cikin ababen zargin da DSS ta kama mai suna Hamisu Tukur wanda Bafulatani ne ya shiga hannu da raunuka na harbin bindiga yayin da ɗayan mai suna Bature wanda shi ma Bafulatani ne ya gamu da ajalinsa.

Ana iya tuna cewa, makonni uku da suka gabata ne wasu gungun ’yan ta’adda ɗauke da makamai suka ka yi awon gaba da mahaifiyar fittaccen mawaƙin yayin wani farmaki da suka kai gidanta da ke ƙauyen Kahutu na Ƙaramar Hukumar DanJa ta Jihar Katsina.

Sai dai bayan kwanaki 20 a hannun maharan Hajiya Hauwa’u Adamu ta shaƙi iskar ’yanci.