Jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kai samame ofishin kungiyar SERAP da ke Abuja.
Hukumar ta kai samamen ne sa’o’i bayan da jamianta suka kame Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta (NLC), Joe Ajaero.
A safiyar Litinin jami’an DSS suka kama Ajaero a filin jirgin sama da ke Abuja, a hanyarsa ta zuwa ƙasar Birtaniya taron Kungiyar Kwadago ta Duniya.
Bayan nan ne SERAP ta sanar cewa jami’an hukumar ta kai samame ofishinta.
- Yadda DSS ta kama shugaban NLC Ajaero
- Ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta
- Matsin rayuwa: Makaho mai shekara 65 ya sa a jefa shi a teku
Duk da cewa babu cikakken bayanin wainar da ake toyawa, SERAP, ta wallafa a shafinta na X cewa: “Jami’an DSS sun zo sun mamaye ofishinmu da ke Abuja ba bisa ka’ida ba, da cewa suna neman daraktanmu.
“Muna kiran Shugaba Tinubu ya umarci DSS nan take su daina razana jama’a da barazana ga ’yancin al’umma.”
A ranar Lahadi kungiyar SERAP ta ba wa Shugaba Tinubu wa’adin awa 48 ya janye karin kuɗin man fetur.
“Muna kira ga Shugaba Tinubu ya yi amfani da matsayinsa ya umarci NNPCL ya janye haramtaccen karin kudin fetur a gidajen manta,” in ji wasikar da Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya sanya mata hannu.