Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta janye dakarunta da ta tura gadin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke da gidan Gwamnatin Jihar da kuma Ofishin Gwamnan.
Jita-jita dai ta yi kamari cewa hukumar ya yanke shawarar daukar matakin ne bayan Gwamnan ya zage ta.
- NAJERIYA A YAU: Asarar Da Najeriya Ta Yi Saboda Rashin Zuwa Gasar Kofin Duniya
- Najeriya ta sami tiriliyan 1.3 ta hanyar noman rake a shekara 10
To sai dai mai magana da yawun Gwamnan, Olawale Rasheed, a cikin wata sanarwa ya ce janyewar na da nasaba ne da ‘kishin’ da ake samu tsakanin jami’an ’yan sanda da na DSS din da aka tura su yi gadin Gwamnan.
Rasheed ya ce matakin lamari ne da ya shafi hukumomin ’yan sanda da na DSS, ba Gwamnan ba.
Sanarwar ta ce, “Muna so mu bayyana cewa an sami wata ’yar rashin fahimta tsakanin jami’an ’yan sanda da na DSS.
“Tuni an kai rahoton zuwa ga hedkwatocin hukumomin tsaron biyu da lamarin ya shafa kuma za su magance ta.
“Muna tabbatar wa jama’a cewa babu wani abun tayar da hankali. Gwamnanku na cikin aminci, kuma harkokin mulki na ci gaba da gudana yadda ya kamata,” inji sanarwar.