Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyaci dakataccen Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hancin da Rashawa (EFCC), Abdulrasheed Bawa.
Bawa ya isa ofishin na DSS sa’o’i kadan da bayan dakatar da shi da Shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar Laraba.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Ya Kamata A Rika Bada Agajin Jini
- Tsawa ta kashe alkalin wasa ana tsaka da kwallon kafa a Neja
“Gayyatar ta shafi wani bincike da ake yi a kansa,” in ji sanarwar da Kakakin DSS, Peter Afunanya, ya fitar a yammacin Laraba.
Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewar da Shugaba Bola Tinubu ya yi na dakatar da Bawa domin ba da damar gudanar da bincike game da ofishinsa kan wasu zarge-zarge.
A cewar sanarwar da Daraktan Yada Labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie Bassey ya fitar, matakin ya biyo bayan zarge-zargen “masu girma” na cin zarafin ofishi da ake wa Bawa.
“An umarci Mista Bawa da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Daraktan Ayyuka a Hukumar, wanda zai kula da harkokin ofishin har zuwa lokacin kammala binciken,” in ji sanarwar.
A makon da ya gabata ne shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Bayan dakatar da Emefiele, DSS ta yi awon gaba da shi a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Jihar Legas.