✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

DSS ta bukaci ASUU ta janye yajin aikinta

Hukumar ta c yajin aikin zai iya yin tasiri ga matsalar tsaro

Hukumar tsaro ta DSS ta bukaci Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) da ta janye yajin aikin da take ci gaba da gudanarwa.

A cewar hukumar, ci gaba da yajin aikin zai iya shafar lamarin tsaro a Najeriya.

Daraktan hukumar mai kula da shiyyar Yobe, Yunusa Abdulkadir, ne ya yi wannan roko a Damaturu, babban birnin jihar, yayin wani taro na daraktocin hukumomin tsaron shiyyar Arewa maso Gabas suka gudanar ranar Alhamis.

Yunusa ya ce, baya ga kassara sha’anin ilimin jami’o’i, yajin aikin ASUUn ka iya barazana ga fannin tsaron kasa.

A cewar jami’in, “Duk da sanin cewa hakkinta ASUU ke nema, amma akwai bukatar ta yi la’akari da yadda aka shafe shekaru da masu yawa yankin Arewa maso Gabas na fama da rashin tsaro.”

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa an shirya taron Darakatocin tsaron ne domin ci gaba da tattauna yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Arewa maso Gabas.