✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS: ‘Babu hannunmu a gayyatar Na’abba’

Fadar Shugaban Kasa ta ce babu kamshin gaskiya a zargin da ake ta yi cewa Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyaci tsohon kakakin Majalisar Wakilai…

Fadar Shugaban Kasa ta ce babu kamshin gaskiya a zargin da ake ta yi cewa Hukumar Tsaro ta DSS ta gayyaci tsohon kakakin Majalisar Wakilai Ghali Umar Na’abba ne saboda wasu kalamai da ya yi kan Shugaba Buhari.

Fadar a wata sanarwa da ta fitar da yammacin Lahadi ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da abun da ta kira ‘yinkurin neman suna’, tana mai cewa zargin ba shi da tushe ballantana makama.

A cikin sanarwar, mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya ce a iya binciken da suka yi, sun gano cewa babu wata alaka tsakanin gayyatar Ghali da Fadar Gwamnatin.

Garba Shehu ya yi kira ga Ghali da ya guji shafa wa Buhari kashin kaji tare da nisanta fadar daga wadancan zarge-zargen.

Ya kuma shawarce shi da ya fi mayar da hankali wajen kare kansa a maimakon tsoma Fadar Shugaban Kasar a abun da bai shafeta ba.

“Akwai ‘yan siyasa na gaske da sukan yi magana kuma Fadar Shugaban Kasa ta mayar musu da martani, akwai kuma ‘yan ku-ci-ku-ba mu masu neman suna ta hanyar kirkirar maganganu don kawai su ja hankalin jama’a,” inji Garba Shehu.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar Juma’ar ce DSS ta ce ta aike wa Ghali Na’abba da goron gayyata domin ya amsa wasu tambayoyi a hedikwatanta.