Rahotannin da ke fitowa sun nuna shahararren dan kwallon Kwaddebuwa da yanzu haka yake kwallo a kulob din Chelsea na Ingia ya kusa yin ritaya daga wasan kwallon kafa.
Kamar yadda dan kwallon dan kimanin shekara 36 ya sanar, ya ce yana sa ram yin ritaya ne a kulob din na Chlsea a karshen kakar wasa ta bana.
“Wannan shekara ina sa ran ita ce ta karshe a tarihin kwallon kafa ta kuma ina fata na samu nasarar lashe kofuna a kakar wasa ta bana a kulob din Chelsea”, a lokacin da yake hira da gidan talabijin na Chelsea a ranar Litinin da ta wuce.
Drogba ya samu nasarar zura kwallaye 160 ga kulob din na Chelsea al’amarin da ya sa ya kasance daya daga cikin ’yan kwallo hudu da suka fi zura kwallaye a kulob din. ’Yan kwallon da ke gaban Drogba a tarihin zura kwallo a kulob din sun hada da Frank Lampard da Bobby Tabling da kuma Kerry Didon.
Drogba zai yi ritaya daga kwallo
Rahotannin da ke fitowa sun nuna shahararren dan kwallon Kwaddebuwa da yanzu haka yake kwallo a kulob din Chelsea na Ingia ya kusa yin ritaya…