✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu

Dakta Doyin Okupe ya rasu ne bayan fama da jinya a sakamakon cutar kansa.

Tsohon Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Dakta Doyin Okupe, ya rasu.

Dakta Doyin Okupe ya rasu ne a asibiti a Legas, bayan fama da jinya a sakamakon cutar kansa.

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da rasuwar Doyin Okupe ta wata sanarwa a safiyar Juma’a.

Doyin Okupe wanda ya rasu yana da shekara 72, gwamnan ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.