✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Donald Trump zai bakunci Sarauniyar Ingila

Fadar Buckingham ta Ingila ta sanar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump zai kai ziyara ta kwana uku zuwa Birtaniya daga ranar 3 zuwa 5…

Fadar Buckingham ta Ingila ta sanar da cewa Shugaban Amurka Donald Trump zai kai ziyara ta kwana uku zuwa Birtaniya daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Yuni mai zuwa.

Shugaban na Amurka da Uwargidansa Melania Trump za su kasance bakin Sarauniya Elizabeth II a yayin bikin cika shekara 75 da Yakin Duniya na Biyu a Portsmouth.Daga nan zai tattauna da Firayi Ministar Birtaniya a Downing Street.

Mista Trump ya taba ganawa da Sarauniyar a Fadar Windsor Castle lokacin wata ziyarar aiki da ya kai a watan Yulin bara. Fadar White House ta sanar da cewa wannan ziyarar da Shugaban zai kai za ta “tabbatar da dangantaka ta musamman da ke tsakanin Amurka da Birtaniya,” kamar yadda BBC ya ruwaito.

Firayi Ministar Birtaniya Theresa May ce ta yi wa Shugaban alkawarin za ta ba shi damar kawo irin wannan ziyarar bayan da aka zabe shi a shekarar 2016, amma ba a sanya rana ba.

Ba kowane ke murna da wannan ziyara da Shugaban na Amurka a Birtaniya ba.

Ministar Harkokin Waje daga bangaren jam’iyyar adawa ta Labour, Emily Thornberry ta nuna damuwarta kan ziyarar “A ranar da wannan mutum ke neman yin watsi da wani kuduri na Majalisar Dinkin Duniya kan amfani da fyade a matsayin matakin yaki, ita kuma Misis May ta gayyace shi ya zo nan a karrama shi,” inji ta

A shekarar 2011, Sarauniya Elizabeth ta karbi bakuncin Shugaba Barack Obama zuwa Fadar Buckingham a 2011.