Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump, ya tsallake rijiya da baya bayan injin jirgin saman da ya dauko shi ya daina aiki a sararin samaniya.
Matsalar da injin din jirgin da ya dauko Trump ya yi saukar gaggawa ne a lokacin da tsohon shugaban kasar ke hanyarsa ta komawa Palm Beach daga New Orleans, inda ya halarci wani taron siyasa da magoya bayan jam’iyyarsa ta Republican.
- Harin asibitin yara ya ja wa Rasha karin bakin jini
- Real Madrid ta kora PSG gida; Man City ta tsallaka zagaye na gaba
A ranar Laraba ne kafafen yada labarai Amurka suna sanar da faruwar lamarin da jirgin alfarmar, wanda ke dauke da Trump da hadimansa.
ciki har da kafar yada labarai ta Politico a Amurka ta bayyana cewa jirgin ya samu matsala ne bayan minti 20 da tashinsa.
Ta bayyana cewa bayan minti 20 zuwa 30 da tashin jirgin, daya daga cikin injinan jirgin ya mutu a sararin samaniya, dole ta sa matukin jirgin ya koma New Orleans.
Washington Post ta ce tsautsayin da ya faru a ranar Asabar, ya taso ne a daidai lokacin da jirgin kirar Dassault Falcon 900 yana daidai Kogin Mexico.
Ta ce jirgin na haya ne da Trump da tawagarsa suka dauki haya zuwa wurin taron.
Amma daga baya an sauya mishi jirgi, tare da ’yan rakiyar tasa suka koma Palm Beach.