✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don samar wa jama’a aiki na shiga harkar sufuri – Alhaji Abdulmunafi

Alhaji Dokta Abdulmunafi Yunusa Sarina shi ne Shugaban Rukunin Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Azman Air Serbices da Azman Oil & Gas kuma daraktan kudi…

Alhaji Dokta Abdulmunafi Yunusa Sarina shi ne Shugaban Rukunin Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Azman Air Serbices da Azman Oil & Gas kuma daraktan kudi na kamfanin sufurin motoci na Sani Brothers Transport LTD. A ttaaunawarsa da Aminiya ya bayyana irin matsalolin da harkar zirga-zirgar jiragen sama take fuskanta a kasar nan da kuma sauran abubuwa. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so sanin takaitaccen tarihin rayuwarka?
Alhaji Abdulmunafi: An haife ni a garin Sarina da ke karamar Hukumar Garko a Jihar Kano. Na yi makaranta a Sumaila Central Firamare daga nan na dawo Kano na ci gaba da karatuna. Ban yi karatun zamani mai zurfi ba, amma na yi karatun Arabiyya sosai. Daga nan na shiga harkar saye da sayarwa. Na dade ina harkar kasuwanci har zuwa yanzu.
Aminiya: Kasancewarka wanda ya dau tsawon lokaci yana kasuwanci tun kana matashi, ya zaka iya kwatanta harkar kasuwanci a da da kuma a yanzu da aka samu ci gaban fasahar sadarwa ta Intanet?
Alhaji Abdulmunafi: A lokutan baya da suka wuce abubuwa ba su ta’azzara da tsada kamar yadda muke ciki a yanzu ba, saboda ada mutum yana iya amfani da karamin jari ya yi kasuwanci har a samu abin alheri, amma yanzu ba ya biyan bukata. Har ila yau, an samu ci gaba musamman ta hanyar sadarwa, inda ada za ka dauki kudinka ka tafi Legas ka yi siyayya, to yanzu an sami sauki, akwai bankuna wanda za ka saka kudinka ka je ka riske su, ko kuma su masu kayan su turo maka lambar asususunsu na banki ka saka musu kudin, idan ta dauro ma ba sai kaje ba, su turo maka kayan, a kawo maka har gida. To wannan ba iya kasar nan ba har kasashen waje idan kaso ba sai kaje ba, ka ga akwai ci gaba sai dai hakan yana bukatar kudin masu yawa sabanin a baya, saboda yanayin zamani ya canza duniyar baki daya.
Aminiya: An fi sanin ka a harkar sufurin manyan motoci da gidajen mai, ya ka yi ka shiga harkar  zirga-zirgar jiragen sama?
Alhaji Abdulmunafi: Ita harkar sufuri gadar ta muka yi tun muna yara, domin mun tashi mun ga iyayenmu da yayyinmu suna yi, sai suka jawo mu, suka nuna mana har suka taimaka mana suka ba mu mota don su ga iyarwarmu. To hakan da suka yi mana sai Allah Ya sa wa abin albarka saboda addu’ar da suka rika yi mana wacce ita take binmu muke ta ci gaba. Tun ina karami ni mutum ne mai son harkar sufuri duk irin wahalhalun da ke cikinsa, sai dai akwai taimaka wa jama’a a cikinsa saboda haka na kudiri niyyar yinta don na taimaka wa jama’a. Na yi sufirin bas-bas, na yi na tasi, na yi na Akori-kura, na yi na manyan motoci masu dakon mai da kaya. Daga nan sai na ce barina bude gidan mai don na sake taimaka wa jama’a, don za ka tarar da mutane suna wayar gari ba su san inda za su nufa ba ga kuma iyali, sai na bar harkar gidajen mai don na ba da gummanwa ta ga al’umma na kuma tallafa wa gwamnati. Don haka za ka samu duk gidan mai daya  akalla yana da ma’aikata 25.
 Ina nan sai na ga cewar bari na leka harkar jiragen sama na ga abin da yake cikinta, duk da mutane suna cewa tana da wahala. A shekarar 2009 na yi rijista da hukumar samar da rijistar kamfanunnuka ta kasa wato (CAC) da sunan Azman Air Serbices, dama ina da Azman Oil & Gas, bayan nan muka nemi izinin gudanar da harkar daga gwamnati don cika ka’ida.  
Aminiya: Wacce irn gudummawa rukunan kamfanoninka suka bai wa jama’a ta fuskar tattalin arziki?
Alhaji Abdulmunafi: Babu babbar gudummawar da ta wuce ka bai wa mutum aikin yi. Misali ina da tireloli da yawa kuma ga gidajen mai da kamfanin zirga- zirgan jirage, ka ga idan ka dauki harkar sufurin motoci kowace mota daya akalla tana tafiya da mutum hudu ne idan sun kai guda 200 ka ga kana da mutane 800. Ban da kanikawa ga masu kula da motocin. Idan ka koma gidajen mai da suke a Kano da Abuja da Bauchi da Sokoto da Minna da Kaduna da sauran garuruwa za ka tarar akwai ma’aikata da dama, akwai gidan man da na bude na dauki ma’aikata 85, sannan a harkar jirage kuma duk inda muke zuwa muna da ofis da ma’aikata. Ina ganin cewar akalla ina da mutane dubu bakwai a karkashina.
Aminiya: Ganin cewar jiragenka suna zirga-zirga ne a iya cikin gida Najeriya, akwai wani kokari da kuke don fara jigila zuwa kasashen ketare?
Alhaji Abdulmunafi: kwarai kuwa don a yanzu haka in Allah Ya yarda ba da dadewa ba za mu kawo jiragen da za su rika zuwa kasashen Afirka ta yamma irin su Nijar da Benin da Ghana da kuma Togo da sauransu. Masu zuwa harkokin kasuwanci wadannan kasashen sai su shirya. Muna da shirin fara tafiye-tafiye a fadin duniya musamman jigilar aikin Umarah a Saudiyya.
Aminiya: Shin rukunan kamfanoninka zai iya ba wa jama’a damar sayen hannun jari, kuma kashi nawa cikin 100 za ku bayar?
Alhaji Abdulmunafi:Yanzu kam ba mu gama tsara ko za mu sayar da hannun jari ga jama’a ba ko kuma a’a, sai mun zauna da mahukuntan kamfanin mun tattauna, shawarar da aka yanke zamu sanar a jaridu, rediyo da sauran kafafan watsa labarai.
Aminiya: Akwai  danganta tsakanin kamfanin Azman da Sani Brothers Transport LTD?
Alhaji Abdulmunafi Kamfanin Sani Brothers shi ne uwa, shi ne uban kamfani Azman. Komai Azman ya zama Sani Brothers ne tushensa. Har ila yau, na yi wa ‘yan uwana godiya da suke bani shawara da goyon baya, Allah ya saka musu da alkhairi
Aminiya: Wane kira za ka yi wa gwamnati akan bunkasa kasuwanci da masana’antu musamman irin na sufurin jiragen sama?
Alhaji Abdulmunafi: Kirana shi ne gwamnati ta farfado da masana’antu ta kuma taimaka wa masu sana’a ta jiragen sama domin irin yadda harkar take cikin barazana, muna kira ga gwamnati da ta shigo ta bamu tallafi don samun bunkasa ta al’umma su samu walwala musamman muna bukatar a rage mana haraji wanda yana da yawa.