Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin kyawawan ayyukan da suka dace ma’aurata su gabatar yayin shagalin murnar Karamar Sallah.
Sunnonin Shagalin Sallah:
Ibada: Mu sani ya ’yan uwa, duk da kasancewar ranar Sallah rana ce ta murna da shagali da jin dadi amma abu mafi muhimmanci a cikin wannan rana shi ne kasancewarta rana ta ibada.
- Ba a ga watan Sallah ba a Saudiyya
- Rarara ya gwangwaje ’yan Kannywood 57 da kyautar 50,000 kowannensu
Don haka ibada ita ya kamata ma’aurata maza da mata su fi bai wa muhimmanci sama da dafe-dafen abinci da shirye-shiryen shagalin Sallah.
Babbar ibada ta farko a wannan rana itace fitar da zakkar fidda kai tunda sassafe, a raba ga mabukata kafin a tafi Sallar Idi, in har aka makara sai bayan an sakko daga Sallar Idi aka bayar to an rasa wannan lada ta zakkar fidda kai.
Babbar Ibada ta biyu a wannan rana itace Sallar Idi, wacce take wajibi ga dukkan Musulmi maza da mata, ba a dauke ma kowa ba sai bisa lalura.
Don haka kuskure ne abinda mafi yawa daga cikin matan Hausawa ke yi na kin zuwa Sallar Idi kawai don yin dafe-dafe da soye-soyen kayan abincin sallah.
Ai zuwa idin nan shi yafi alfanu sama da komi; don haka ne ma a lokacin rayuwar Annabi (SAW) matane ke zuwa filin idi har mata masu jinin haila Annabi (SAW) Ya Umarcesu da zuwa wajen da ake Sallar Idi amma su tsaya daga baya.
Haka har macen da bata da hijabin da zata rufe jikinta, Annabi (SAW) Ya umarceta da ta nemi aron na ’yar’uwarta ta tafi wajen Sallar idin.
Wannan duk yana kara nuna mana matuqar muhimmancin zuwa Sallar Idi ga kowane musulmi ba wai maza da qananan yara kadai ba. Don haka duk wata uwargida Musulmar kwarai ta tabbatar ta karasa duk wani aikin abincinta kafin lokacin zuwa idi; in kuma ba halin haka to sai tayi hakuri sai ta dawo ta karasa domin zuwa idin nan yafi komi muhimmanci a wannan rana.
Daga cikin kyawan sunnonin da Annabi (SAW) Yake gabatarwa kafin tafiya Sallar Idi sun hada da: Yin wanka; yin asuwaki; sa sabbin kaya ko mafi kyawo daga cikin tsofaffin; sanya turare; cin mara ta dabino, watau 3, 5 ko 7; sai kuma canza hanyar dawowa gida, watau hanyar da aka bi aka je masallacin idin, sai a canza a bi wata daban wajen dawowa gida in
da halin yin haka.
Sadaka: Haka kuma yana daga cikin ibadodin murnar Sallah yin sadaka ga talakawa da mabukata; domin Annabi
(SAW) yayi umarni da yin hakan ga taron mata bayan idar da sallar idi, sai yayi masu wa’azi kuma ya umarce su da bayar da sadaka; kuma take suka bi wannan kyakykyawan umarnin na Manzon Allah (SAW), inda suka runka ciro gwala-gwalensu suna bayarwa sadaka saboda Allah.
Don haka ya ‘yan uwa ma’aurata, musamman mata, muyi kokarin yin koyi da wannan Sunnah ta Manzon Allah (SAW)ta hanyar bayar da sadaka a wannan rana ta shagalin babbar Sallah.
Ba dole sai mutum ya wadata sosai ba sannan zai yi sadaka, indai mutum ya yi ta da kyakykyawar niyya to Allah Madaukakin Sarki kuwa zai cika masa ladarsa.
Misali kamar mutum ya bayar da sadakar kudi ga Masallacin unguwarsu; ko ya sayi batirori don sawa a lasifikar masallacin; ko katuwar fitila mai haske sosai; tabarmi, butoci da sauransu.
Ko taimakon wani mabukaci, ko taimaka ma gidajen maruya da kudi, sutura ko
kayan abinci. Ko sayen magani ga marasa galihu a asibiti, da sauran kyawawan ayyuka da mutum ya ga sun dace sai ya aikatar don dacewa da wannan kyakykyawar Sunna ta Manzon Allah (SAW).
Ranar Murna: Abu na hudu mafi muhimmanci a wannan rana shine kasancewarta ranar murna ranar shagali da shakatawa.
Don haka yana da kyau kowane musulmi yin murna a wannan rana, ta hanyar jin ta cikin zuciya, da bayyanar da ita a fuska, da kokarin sa ‘yan uwa da maiwabta cikin nishadi ta hanyar kyakykyawar gaisuwa mai cike da raha, kalmomin kyautatawa da kuma yin abubuwan kyautatawa da jinkai ga kowa a wannan rana.
Haka nan ya halatta yin wakokin nishadi masu dauke da kyawawan kalmomi, musamman mata da yara kanana, Sunnah ce mai kyau su aikatar da wannnan a ranakun murnar Sallah.
Misali, yana da kyau a tara yaran unguwa a gabatar da wani abun wasa da jin dadi wanda zai sanya su cikin murna da farin cikin zuciya; ko macen aure ta tara ’yan matan unguwa su yi wasannin gada ko wakoki cikin wasa da dariya da raha, wannan duk ayyukan alherine wadanda in mutum ya aikata su zai samu lada ga kuma nishadi da jin dadin da zai ji a zuciyarsa.
Ranar Soyayya: In muka bibiyi Sunnonin Manzon Allah (SAW) zamu ga cewa, ranar idin Sallah rana ce ta soyayya da romansiyya da kyautatawa tsakanin ma’aurata.
Kamar yadda aka ruwaito Uwar Mumunai Aisha Radhiyallahu Anha ta ce, a ranar wata idin, ya kasance mutanen Habasha suna wasa da sulke da mashi a harabar Masallaci, sai Annabi (SAW)Ya katangeta da jikinsa, ta yadda kumcinta yana bisa kumcinSa kuma ya yi ta jiran ta har sai da ta kalla ya ishe ta.
Wannan darasi ne mai kyau kuma abin koyi ga ma’aurata ta yadda za su sadaukar da lokacinsu wajen nuna kauna da kulawa ga junansu a wannan rana ta idi.
Don haka yana da kyau ga duka maza da mata suyi wani abu na sadaukarwa da nuna kulawa ga junansu ranar Sallah don su dace da wannan kyakykyawar Sunna kuma su ji dadi da nishadin da ke cikin kyautatawa ga juna.
Sauran kyawawan ayyuka a wannan rana ta Sallah sun hada da kure adaka wajen kwalliya da kuma yawon sada zumunci ga ’yan uwa da abokan arziki.
Da fatan Allah Ya sa a yi shagalin Sallah lafiya, Amin.