Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga cigaban bayani daga inda muka kwana kan ingantattun hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi don samar da kyakykyawar tarbiyya ga ’ya’yansu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
In Jariri Ya fara Tasawa: Watau lokacin da ya fara wayau, yana gane iyayensa da sauran ’yan gidansu, yana nuna karsashin murna lokacin da ake masa wasa, ya fara son ya ci abinci, da sauran sababbin dabi’o’in da suka bayyana. Ga irin yadda ya kamata mahaifiya ta cigaba da jagorantar tarbiyyar jaririnta a wannan lokaci:
1. Ci gaba da bin Ka’idar Jadawalin Kulawa: Kamar yadda muka fada a satin da ya shige cewa sai an rika canza Jadawalin kulawa a kai-a kai akalla duk bayan wata uku, jariri na girma ne dabi’unsa da lokutan da yake bukatar kulawa na canzawa, don haka jadawalin farko ba zai yi amfani sosai ba dole sai an canza shi. A wannan lokaci ma uwa sai ta yi nazarin wadannan sabbin canje-canje na sati daya, lokacin barci da tashin jariri, lokacin ba-haya lokacin da ya fi kazar-kazar da lokacin yawan rigima, sai ta yi amfani da bayanan da ta tattara ta sake wani sabon jadawalin kulawar. Kar uwa ta kasa ci gaba da yin jadawalin kulawa ko ta dauka bai da wani muhimmanci, in ta daure tana yi jaririnta komai bisa ka’ida kuma a kan lokaci, wannan zai kara masa natsuwa da aminci cikin zuciyarsa kuma zai sa ya tashi da wannan kyakykyawar tarbiyya ta yin komai bisa ka’ida kuma a lokaci mafi dacewa. Haka uwa za ta daure ta yi ta yi har zuwa lokacin da ta yaye jaririnta da ma bayan nan.
2. Gabatar masa da mafi muhimmanci al’amura: Da zarar yaro ya fara tasowa, ya fara fahimtar kananan abubuwa, ba yawan wasa, ba wai sa shi dariya kadai za a gabatar masa ba, tun a wannan lokacin za a fara gabatar masa da kyawawan ladubban da za su kawata halayyarsa. Kamar yadda muka fada a baya cewa kodayaushe aka zo daukarsa a yi masa sallama tare da kyakykyawan murmushi, a shayar ko ciyar da shi tare da farawa da Bismillah, a kwantar da shi tare da addu’o’in kwanciya barci, haka wajen sa kaya da wanka duk a karanta masa azkar na gabatar da wadannan ayyuka, sannan da addu’o’in neman tsari na safe da maraice.
Abu mafi muhimmanci a wannan lokacin shi ne a gabatar wa da yaro Mahalliccinsa Allah Subhanahu wa Ta’ala. Yawancin uwaye da yaronsu ya fara tasawa burinsu shine ya iya fadar kalmar baba da mama, mafi alfanu ga rayuwar yaro shine ya fara sanin Mahalliccinsa Allah Madaukakin Sarki, a rika yawan fada masa sunayen Allah ana nuna samaniya, a rika yawan fada masa kalmash shahada, da karanta masa kananan surori na Al’kurani Mai Tsarki, da sauran dukkan wasu kyawawan ayyuka da aka fahimci za su sadar da shi ga Ubangijinsa, su dasa shukar kauna da shaukin Ubangijinsa tun a farkon rayuearsa.
Bayan nan abu na biyu mafi muhimmanci da ya kamata iyaye su gabatar ga dansu lokacin da ya fara tasawa shi ne koya masa da sabar masa son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, wannan abu ne mai matukar muhimmanci domin ba wanda imaninsa zai cika har sai ya ji yana son Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam sama da son da yake wa iyayensa, ’ya’yansa da shi kanshi. Don haka in iyaye suka sabar wa dansu da wannan kyakykyawar dabi’a tun yana karami zai tashi da shaukin son Manzon Allah da kokarin koyi da shi cikin al’amuran rayuwa.
Mahaifa za su iya gabatar da haka ga karamin dansu ta hanyar wasanni da raha, kamar in aka yi masa wasa ya yi murmushi sai a ce ‘yawwa wane, ka rika yawan murmushi domin wannan dabi’ar Annabi Sallallahu alayhi wa Sallam ce. Koda bai fara fahimtar magana ba haka za a yi ta yawan fadan sunan Annabi Sallallahu alaihi wa Sallam hade da kyawawan halaye da dabi’o’insa ga yaro har su zauna a cikin kwakwalwarsa. In kuma ya fara fahimtar magana sai a fara ba shi gajerun labaran Fiyayyen Halitta Sallallahu alaihi wa Sallam cikin siga mai saukin fahimta daidai da hankalinsa. Haka kuma a saba wa yaro son da Sahabban (Radhiyallahu anhum) Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam domin su ne mafi kyawun abin koyi kuma abin riko bayan Manzon Allah Sallallahu alaihi wa Sallam.
Haka nan iyaye za su tafi da wannan salo na tarbiyya ba tare da gajiyawa ko sakaci ba har zuwa lokacin da dansu zai mallaki hankalin kansa, in dai suka rike wannan, su kansu sai dansu ya burge su saboda nagartarsa balle kuma sauran jama’a.
Sai sati na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawar Sa a kodayaushe, amin.