Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Ga cigaban bayani daga inda muka kwana kan ingantattun hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi don samar da kyakykyawar tarbiyya ga ’ya’yansu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin..
Tarbiyya Lokacin Jarinta, cigaba…
7. Abubuwa mafi muhimmanci: daga cikin sauran abubuwa mafi muhimmanci da ya kamata uwargida ta yi tsayin-daka wajen gabatar da su bisa ka’ida a lokacin jarinta:
Tsabta: Kamar yadda bayani ya gabata game da kiyaye lokutan barci da shayarwa, to haka nan yana da matukar muhimmanci mahaifiya ta sa ido sosai ga tsabtar jaririnta, kar ya kasance tana barinsa cikin kazanta da rashin tsarki, da kin ga ya yi datti in mai bukatar wanka ne nan da nan ki yi masa wanka, in kuma mai bukatar a canza masa tufafi ne ko a goggoge sai ki yi masa. Kar ki yi rowar ruwa wajen yi masa tsarkin fitsari da na ba-haya. Yana da kyau bayan tsarkin ba-haya kuma ki sa sabulu ki wanke masa wannan bangaren. Haka nan kula da tsabtar sauran sassan jikinsa, ki na yin buroshi irin jarirai ki rika goge masa kufan nono daga bakinsa da dasashinsa, wannan ba kullum ba duk lokacin da kika lura bakin yana bukatar gogewa. Haka nan hancinsa ki rika yawan lekawa, in majina ko tasono sun taru ki fitar domin barinsu na iya hana shi shakar numfashi yadda ya kamata, hakan kuma na iya haifar masa da rashin lafiya. A kula kuma kar a wuce wuri wajen tsabta, yawan wanka da jika jariri fiye da kima na iya sa sanyi ya kama shi, haka kuma yi masa wanka da ruwan sanyi musamman in ba a lokacin bazara ba ne, hakan nan yawan kwalkwulen datti a hanci, baki ko kunne na iya shigar da wasu kwayoyin cuta da ka iya kwantar da shi. A kula sosai wajen wanka kar a bari ruwa ya shiga kunnuwa, baki ko hancin jariri. Haka nan kayan kiyaye tsabta irinsu sabulu, man shafawa, hankicin goge-goge da sauransu, a tabbatar an zabi masu kyau wadanda ba su da yawan sinadarai masu zafi da ka iya cutarwa ga fatar jariri.’
Kamar yadda muka fada a baya, yana da matukar alfanu komi uwa za ta gabatar na kulawa ga jaririnta, ta fara da Bismillah, wadanda kuma suke da adhkar na musamman kamar sa kaya, sa sabbin kaya, shayarwa, barci da sauran sai ta fara da karanta wannan adhkar din. Wajen wanka da yin tsarki kullum ta rika gabatar da adhkar din shiga kewaye, in ta gama kuma na fitowa daga kewaye. Wannan tana saukaka wa kanta wasu matakan tarbiyya ne nan gaba, jariri ya saba jin wadannan kyawawan kalamai lokacin gabatar da wannan al’amura, don haka za su yi masa saukin dauka da aiwatarwa lokacin da ya kara tasawa.
Kiyaye Lafiya: Haka nan yana daga cikim abubuwa mafi muhimmanci uwa ta sa ido sosai ga lafiyar jaririnta. Da farko tabbatar da tsabta da cikakkiya kuma kyakykyawar kulawa suke samar da ingantacciyar lafiya ga yaro. Haka nan lafiya da koshin mahaifiya su ma suna tasiri ga lafiyar jariri, sannan tsabta da kiyayewa ga abubuwan da ke isa ga jariri ba masu illa ga lafiya ba ne, musamman masu isa ga fatar jiki ko daya daga cikin kofofin jiki. Yawan kuka, yawan rigima da fisge-fisge, alama ce ta cewa wani abu na damunsa. Haka nan yawan barci, rashin kazar-kazar, kin shayarwa, yawan tsufa, yawan zubar majina ko miyau duk alamun cewa jariri ba ya jin dadi, don haka sai a yi hanzarin nema masa magani. Yana kuma daga cikin kulawa da lafiya bin ka’ida wajen bada magani, da takaita yawan bada maganin sai ya zama dole domin magungunan zamani yawancinsu suna da tasirin bayan alfanu wanda yawanci illarsu ba ta bayyana sai bayan tsawon lokaci. Haka nan yana daga cikin kula da lafiyar jiki, zuciya da ma’aikatar hankali iyaye su tanadi magunguna masu albarka irin su ruwan zam-zam, man zaitun, man bakin algarib da sauransu su rika amfani ga jaririnsu daidai da bukata.
Sai sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.