✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Don Ma’aurata: Bayani kan tarbiyya (10)

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga…

Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.

Ga cigaban bayani daga inda muka kwana kan ingantattun hanyoyin da ya kamata ma’aurata su bi don samar da kyakykyawar tarbiyya ga ’ya’yansu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin. 

 

Tarbiyya Lokacin Jarinta, cigaba… 

6. Taka-tsan-tsan Da Haramtattun Abubuwa: Duk iyayen da fatan samun zuriyya dayyiba, da fatan samun da nagari, wanda zai amfane su, ya amfani kansai kuma ya amfani alumma, to dole sai sun yi tsayin- -daka wajen kiyaye haramtattun abubuwa isa gare shi ta kowace hanya, mafi muhimmanci ta hanyar abinci, abin sha, sutura. da sauran kayan masarufin da ake amfani da su wajen kula da shi a tabbatar ta hanyar halal aka samar da su ba ta haramtacciyar hanya ba. Dole iyaye su yi kokarin raba kansu da dabi’ar zamanin nan ta ya ki halal ya ki haram, watau halal da haram ya zama duk matsayin su daya, duk wanda aka samu ci ake. 

Sannan ba ta wajen abinci da sauran kayan masarufi ba kadai, haka nan iyaye su yi kokarin kiyaye munanan dabi’u ga isa zuwa ga kunnuwa, idanuwan da hankulan yaransu tun farkon lokacin Jarinta har zuwa lokacin da zasu mallaki hankalin kansu. Don haka yana da matukar alfanu su iyayen su zama masu kyautata dabi’unsu a kowane lokaci, sannan su zama masu kyautata zamantakewarsu da dangantakarsu. Su yi tsayin-daka ganin cewa yasashshiyar magana, kama zagi da batsa da karyace-karyace ba su isa ga kunnuwan jaririn dansu, haka nan wake-waken zamani masu cike da shirme a kiyaye isar da su ga yaro tun daga jarinta har zuwa cikar kamalar hankalinsa. Maimakon haka sai a kewayesa da kyawawan dabi’u da karatun kur’ani da ambaton Allah Madaukakin Sarki. Yin hakan zai tsarkake masa hankali, ya saukar masa da natsuwar ruhi Ya kuma kare shi daga rudu da hargitsin da shaidan ke haifarwa cikin kwakwalwar bil adama. 

7. Abubuwa mafi muhimmanci: Daga lokacin da aka haifo jariri har zuwa wata shida na rayuwarsa a duniya, abubuwan da ya fi bukata sama da komai a wannan lokacin shi ne ingantacciya kuma cikakkiyar kulawa ta bangaren tsafta, ciyarwa, shayarwa, kula da sutura, barci da kuma lafiya. Sakaci ga daya daga cikin wadannan na iya haifar da matsala ga lafiyar jiki ko ta ma’aikatar hankalin jaririn. Don haka iyaye, musamman uwa sai ta dage ta ladabtar da kanta wajen kula da wadannan muhimman abubuwa. In ta riga ta saba kanta kuma ta saba jaririn, sauran watanni renon danta za su zo mata da matukar sauki kwarai da gaske. Ga wasu hanyoyi da za su taimaka uwargida wajen bayar da cikakkiyar kulawa ga jariri a farkon jarintarsa:

*Ta horar da kanta wajen kiyaye lokutan barcinsa, ta samu wani dan karamin littafi kullum ta rika rubuta lokacin da ya yi barci da kuma lokacin da ya farka, in ta yi haka na sati daya za ta fahimci yanayin barcinsa, lokacin barcinsa da kuma barcin awa nawa yake yi a rana, wannan zai saukaka al’amuran gareta domin kodayaushe tana sane da lokacin da danta zai bukace ta don haka za ta zama cikin shirin ba shi kulawa a wannan lokacin. Sannan in ta fahimci lokacin barcin danta, ta yi kokarin ta samar masa natsatstsen yanayin da zai yi barcinsa a daidai wannan lokaci kullum ba tare da canji ba. 

*Haka wajen ba da abinci, ta horar da kanta wajen shayar da shi sau 3 kadai a rana, a nan ina nufin shayarwar da za ta kosar da shi ba shayarwa ta rarrashi ko ta don a samu ya yi barci ba. Jariri yana bukatar shayarwa kod yaushe, domin tsotson nonon mahaifiyarsa ba kosar da shi kadai ne aikinsa ba yana kuma saukar masa da natsuwa da kawar da damuwarsa da kuma tabbatar masa cewa yana da mai kula da shi. Don haka ba kodayaushe ne aka tashi shayar da yaro za a cika masa ciki fam ba har ya kasance yana amansa. Sai dai a kintaci lokuta guda uku a rana sai a zauna a bashi ya sha sosai har sai ya koshi, kuma lokutan nan ya kasance ba canji kullum a daidai wannan lokaci sai a shayar da yaro. Yana da kyau a hada lokacin wanka da shayarwa da barci lokaci daya. Misali da safe kar a shayar da shi ya koshi sai an masa wanka, daga nan sai a shayar da shi, dama lokacin barcinsa ne don haka yana koshi sai barci ya kwashe shi. Ta haka jariri ba zai rika yawan koke-koke da rigimar yunwa ko rashin samun cikakkiyar kulawa ba.

Sai sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.