A wata tattaunawa da Shugaban UBEC ya yi da wani dan uwansa, an jiyo shi yana cewa duk inda za a nemo kudin, a je a nemo domin a biya kudin fansansa da ’yarsa da aka yi garkuwa das u jiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
A cewarsa, “Don Allah ku hanzarta. Lokaci na kurewa. Idan aka yi magana ka ga zai dauki wani dan lokaci kafin inda za a yi mhada a karba, kuma wannan abu ne in Allah ya yarda ana so a gama cikin awa guda. Don Allah su tartara duk abin da za su tattara cikin awa daya.”
Sai wanda suke maganar da shi y ace, “Ana hadawa. An kara hada kusan miliyan 13 cikin daren nan. Dare ne matsalar. Wani ya min alwakarin zuwa safiya zai ba ni miliyan 60. Da za su karbi dala, da mun ba su yanzun nan. Wallahi ba mu da Naira. Mun samu miliyan biyu wajen wani. Ka fada musu muna kokarin hada kudin.”
Sai Shugaban UBEC din ya kara da cewa, “Amma wanda aka ce an samu daga Abuja, na san zai yi wuya a kai kudi daga Abuja zuwa Kaduna a daren nan. Ga 30 (miliyan ken an yake nufi) a kasa, ga 13 yanzu ya zama 43 ke nan. Suran 17. Don girman Allah duk inda za a samu a nemo.”
Sai wanda suke wayar da shi ya ce, “Ka musu bayani cewa ba mu so mu kira mutane da yawa kada abin ya yadu ne.”
Sai ya kara da cewa, “To don Allah a nemo. Yarinyar nan ta ji ciwo a kafa, amma su da kansu suke rike ta. Ba su mana wani abin rashin daidai ba. Suna kula da mu sosai. Abin da aka samu a je a mika wa Hussaini, sannan sauran su biyo.”