✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dolo na 5

Wani Bakano ne ya je wajen farkarsa a Marabar Jos, suna zaune tare a daki sai ta tashi ta shiga wanka, ta bar wayarta a…

Wani Bakano ne ya je wajen farkarsa a Marabar Jos, suna zaune tare a daki sai ta tashi ta shiga wanka, ta bar wayarta a dakin. Yana nan sai aka bugo waya, ya duba sai ya ga an rubuta sunan mai kiran da: ‘Sakarai Na daya.’ Ganin haka sai ya ce bari ya duba lambarsa ya ga da wane suna aka aje ta. Sai ya ga an rubuta: ‘Dolo Na 5.’ Dayake layi biyu gare shi, sai ya sake duba daya lambar, sai ya ga an rubuta: ‘diban Ruwan Tire.’ Da farkar tasa ta dawo daga wanka, shi kuma sai ya tashi tsaye zai fita daga dakin, ya ce mata: “Bari dolo na biyar da diban ruwan tire ya wuce!”

Daga Iliyas Idris Fahad Suleja, 07086228845