Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce dole jam’iyyarsu ta PDP ta karbi mulkin kasar nan don ta magance yadda jini yake kwarara a cikinta.
Wike, wanda ya bayyana hakan a Kaduna lokacin da ya ziyarci tsohon Gwamnan Jihar kuma tsohon shugaban PDP na kasa, Sanata Ahmed Makarfi, a ranar Litinin, ya kuma yi kira ga ’ya’yan jam’iyyar da su hada kansu gabanin zaben 2023.
- Kotu ta daure Sadiya Haruna ba tare da zabin tara ba
- Ronaldo ya zama mutum na farko da ya samu mabiya miliyan 400 a Instagram
Sai dai Gwamna Wike ya ce ba ziyarar siyasa ce ta kai shi ba, ya je ne don ya gaishe da Makarfin wanda kwanan nan ya dawo daga ganin likita a kasar waje.
A cewarsa, “Makarfi kusa ne kuma yana da matukar kima a idanun ’yan PDP saboda salon shugabancinsa da kuma yadda ya ceto PDP a lokacin da aka so yin amfani da Ali Modu Sheriff wajen karya ta.”
Ya ce dole sai ’ya’yan jam’iyyar sun tashi tsaye kafin su iya kwace mulkin kasar nan daga hannun APC a zabe mai zuwa.
A nasa bangaren, Sanata Makarfi ya shaida wa Gwamna Wike cewa ’yan Najeriya ba za su ji dadi ba idan ’yan PDP suka gaza hada kansu don su kwace mulkin.
Ya ce la’akari da sakamakon zaben da ake samu a sassa daban-daban na Najeriya, alamu na nuni da cewa ’yan kasar sun gaji da salon mulkin na APC.