Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya ce dole ne shugabanni su hada kai domin yakar ta’addanci a kasar.
Lawan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da jawaban maraba ga ‘yan majalisar da suka dawo daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara a ranar Talata.
- El-Rufai ga Gumi: Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba
- Dole ne Buhari ya farga don dakile rikicin kabilanci a Najeriya — Dokta Ardo
- Fadar Shugaban Kasa ta fara nazarin sake rufe iyakokin Najeriya
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
“Wajibi ne shugabanni su hada kai don yakar miyagun laifuka dake neman zama ruwan dare. Sannan dole a kawar da son kai da wariya a zukatan mutane,” cewar Lawan.
Lawan ya ce majalisar za ta hada kai da dukkanin matakan gwamnatin don kawo karshen matsalar tsaro.
“A matsayinmu na ‘yan majalisa ya kamata mu yi dokar da za ta magance matsalolin da ke haifar da rikici tsakanin mutanenmu.”
“Za mu tattauna tare da kulla yarjejeniya da matakan gwamnati daban-daban don samar da mafita mai dorewa,” in ji Sanata Lawan.
Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani don bunkasa hadin kai da ‘yan uwantaka tsakanin ‘yan kasar.
Lawan ya kara da cewa kudirin dokar Man Fetur (PIB) ta 2020, da kundin tsarin mulkin kasa na shekarar 1999, zai bunkasa kudaden shiga ga Najeriya tare da tabbatar da yin gaskiya a Ma’aikatar Man Fetur ta Kasa.
Dangane da kokarin gwamnatin tarayya kan samar da allurar rigakafin cutar COVID-19 a Najeriya, Lawan ya ce majalisa ta yi tanadi kan kasafin kudi na 2020 da 2021 kan yadda za a dakile tasirin cutar a karo na biyu.
Kazalika, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta sayo rigakafin allurar karkashin kulawar hukumar NAFDAC.