✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole ne mu yaki dokokin da suka saba wa auren jinsi –Theresa May

Firayiministar Burtaniya, Theresa May, ta yi kira ga Najeriya da dukkan sauran kasashen kungiyar rainon Ingila ta Commonwealth da su rumgumi auren jinsi daya. Tana…

Firayiministar Burtaniya, Theresa May, ta yi kira ga Najeriya da dukkan sauran kasashen kungiyar rainon Ingila ta Commonwealth da su rumgumi auren jinsi daya. Tana mai cewa bai kyautu a ce akwai wasu dokoki da ke maida auren jinsi daya laifi ba a cikin kafatanin kasashen da Ingila ta raina ba.

Theresa May ta bayyana haka ne a rukunin farko na taron shugabannin kungiyar rainon Ingila ta Commonwealth a ranar Talatar da ta gabata. Tana mai cewa sam bai dace a ce an samu wata doka da ke maida auren jinsi haramtacce a kasashen kungiyar rainon Ingila ba.

Fira-Ministar ta ci gaba da cewa tana sane da cewa yawancin dokokin da ke hana auren jinsi daya a tsakanin kasashen da kasarta ta raina, kasar tata ce ta kafa su. Ta kuma kara da fadin cewa, sanya wadancan dokokin a wancan lokacin kuskure ne, sannan a yanzun ma kuskure ne.

“A duk fadin duniya, dokokin da ke nuna bambanci wadanda aka kafa shekaru da yawa, sun ci gaba da shafar rayukan miliyoyin matasa. An maida auren jinsi daya ya zamto laifi, sannan an gaza samar da kariya ga manyan mata da kanana.” 

“Ina da matukar sanin cewar wadannan dokokin kasata ce ta samar da su; kafa su kuskure ne a wancan lokacin, sannan a yanzun ma za su ci gaba da zama kuskure.

“A matsayina na firayi ministar Ingila, ina matukar bakin cikin cewar wadancan dokokin kasata ce ta gabatar da su tun da farko. A matsayinmu na iyali daya, dole mu girmama yanayin rayuwa da al’adar juna. Amma dole mu aiwatar da hakan ta hanyar tsayawa akan nuna daidaito tsakanin mutane, kamar yadda ya bayyana sarari a daftarin kungiyar rainon Ingila.”

Ta kuma kara da cewa, “Ba wanda ya cancanci fuskantar bambanci ko kuma takura saboda yadda rayuwarsu take ko kuma wadanda suke so. Dan haka Ingila a shirye take da ta taimakawa dukkan wani dan kungiyar rainon Ingilar da yake burin sauya fasalin wannan tsohuwar dokar da ta kawo nuna bambanci da kyamar juna a tsakaninmu,” in ji ta.