A yayin da wadansunmu da ke nesa suke share hawayensu saboda juyayin abin takaicincin da ya faru a Benisheikh ta jihar Borno a kwanakin baya, su kuwa wadanda bala’in ya shafa yanzu ne hawayen nasu yake kara kwarara, matan da suka rasa mazajensu har yanzu suna zubar da hawaye su kuma wadanda suka rasa gidajensu suna kokarin yadda za su saba da sabon yanayin rayuwa da suka tsinci kansu a ciki.
Har yanzu muna mamakin yadda aka yi irin wannan kisan gillar a garin Benisheikh, kamar yadda muka yi mamakin irin wannan kisan gillar da aka yi a garurruwan Bama da Baga da Mamudo, domin dukkansu sun jefa shakku a zukatan jama’a. Su wane ne wadannan mugayen ‘yan bindiga da suke kashe mutane kuma su bace a neme su a rasa kamar wadansu aljannu?
Ta yaya suke iya gudanar da wannan mugun aikin nasu, alhali wadannan wuraren da abin ya faru suna karkashin dokar ta-baci ne da ya kamata a ce suna karkashin tsauraran matakan tsaro fiye da ko’ina? Yaya aka yi suke tafiya a cikin ayarin motoci tare da muggan makamai kuma a mafi yawan lokuta a cikin kayan sojoji amma jami’an tsaro na ainihi da aka tura yankin domin su yake su suka kasa ganinsu? Hankali ba zai dauka ba a ce ‘yan bindiga sun yi wa mutane 160 mazauna garin Benisheikh da matafiya kisan gilla kuma babu wanda ya gansu a cikin jami’an tsaro.
Sai dai idan bayanin da wani soja da aka hadu da shi a banki a Damaturu ya yi wa jaridar Dsaily Trust ta ranar 19 ga watan Satumbar nan shi ne kadai hujja, inda ya ce, bai san yadda aka yi ya tsira ba lokacin da ‘yan bindigan suka fado musu bagatatan suka kwace makamansu. Shin ya kamata a ce soja ya zauna ba a cikin shiri ba a yanayi irin na yaki da masu tayar da kayar baya a wurin da ya zama fagen fama kamar yankin Arewa maso Gabas har abokan gaba su ci dununsa? Yaya za a ce an ci dunun soka alhali kamata ya yi a ce yana zaune cikin shiri dare da rana domin fuskantar abokan gaba?
Wani abin kunyar da sojojin suka yi shi ne bayanin da aka yi cewa wadansu sojojin da aka yi zaton an kashe su sun sake bayyana jiya, ashe sun gudu ne suka buya da suka ga makamansu sun kare. To yanzu dai rashin zamansu a cikin shiri da tserewa da suka yi domin su buya ya jawo asarar rayuka 161 na mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da kuma dimbin mutanen da suka rasa muhallansu wadanda suka zama ‘yan gudun hijira a garinsu. Tun da an kona shaguna masu yawa a garin an mayar da mutane da dama matalauta ke nan.
Abin tambaya a nan shi ne, yaya za a yi har jerin gwanon motoci 20 shake da mutane da makamansu su fada wa gari irin Benisheikh da ke bakin hanya, su kashe mutane, su kona garin, amma babu abin da ya same su?
Watanni hudu ke nan da al’ummomin jihohin Yobe da Borno (Adamawa ma ta dan dandana) suke fama da dokar ta-baci, amma har yanzu babu wata nasara da za a iya cewa dokar ta samu wajen magance ta’adin masu tayar da kayar baya, kullum abin da kawai muke ji shi ne kisan gilla, kamar wanda ya faru kwanan nan a Benisheikh. Kodayake za a iya cewa an samu kwanciyar hankali a garin Maiduguri, amma idan an bar gari an koma kauyukan da ke kewaye da gari ai ba za a ce an samu nasara ba.
Saboda haka dole ne gwamnatin tarayya ta janye dokar ta-bacin da ta kakaba wa jihohin Borno da Yobe domin matakan tsaron da aka dauka ba su biya bukata ba. Mutane za su fi samun damar kare kansu idan suna zirga-zirga ba tare da tukurawa ba, domin za su samu damar daukar wa kansu matakan da suka dace.
Yanke hanyoyin wayoyin sadarwa da aka yi tun da aka kakaba musu dokar ta-baci ya taimaka kwarai wajen haifar da kashe-kashen da suka faru, domin idan mutane suka samu damar sanar da ‘yan uwansu game da wani hadari da yake tafe za a iya tsirar da rayuka da dama, amma a yau mutane suna tafiya ne su fada wa halaka da kansu saboda babu wanda zai iya sanar da su abun da ke faruwa.
A yayin da gwamnati da kuma hukumomin tsaro suke kokarin bankado yadda aka yi kisan gilla a garin Benisheikh, wannan filin yana ganin dole ne a tabbatar an hukunta wadanda suka yi sakaci har hakan ta faru. Idan gwamnatin tarayya ba za ta iya hukunta kowa ba game da wannan al’amarin, to kamata ya yi wadannan jiga-jigan jami’an tsaron su mutunta kansu su yi murabus, mutanen su ne, Mai bai shugaban kasa shawara ta fannin tsaro da Babban hafsan tsaro da babban hafsan sojojin kasa. Alhakin abin da ya faru a Benisheikh yana wuyan wadannan mutanen uku ne, domin su ne suke bai wa gwamnati shawara kuma suke kula da tsaro a yankunan, kuma su ne suke bai wa sojojin da suke yaki da masu tayar da kayar baya a karkashin rundunar tsaro ta hadin gwiwa makamai. Tun da sojojin sun ce sun gudu ne saboda rashin makaman kirki, abin da ya janwo aka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, dole ne wani ya dauki alhalin wannan tu’annatin.
Haka kuma dole ne wani ya dauki alhakin yadda aka yi ‘yan bindingan suke amfani da kayan sojoji iri daya da na sojojin rundunar tsaro na hadin gwiwa tun lokacin da aka kakaba wa yankunan dokar ta-caci watanni hudu da suka gabata, ba tare da an ji wata sanarwa daga jami’an tsaro da ta nuna cewa wadansu kayan sojoji sun bace ba. Sai dai idan wadannan ‘yan bindigan ba masu tayar da kayar bayan da ake fada ba ne, kamar yadda wadansu ke gani, dole ne kuma wani ya yi bayanin yadda wadannan ‘yan bindingan suka samu kayan soja da kuma muggan makamansu.
Dole ne a hukunta wadansu dangane da abin da ya faru a Benisheik
A yayin da wadansunmu da ke nesa suke share hawayensu saboda juyayin abin takaicincin da ya faru a Benisheikh ta jihar Borno a kwanakin baya,…