Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya yi kira ga Gwamnoni da su hada kai da Gwamnatin Tarayya wajen yaki da talauci a Najeriya.
Shugaban, wanda ya yi wannan kiran lokacin da ya karbi Gwamnonin Najeriya a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba, ya ce yawan talaucin ba abin da za a lamunta ba ne.
- A karon farko cikin shekara 17, an yi mako 2 ba ruwan sama a Denmark
- NYSC ta tura wa mai yi wa kasa hidima dubu 330 bisa kuskure
Tinubu ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da su manta da bambance-bambancensu su hada gwiwa wajen kakkabe talauci a Najeriya.
Ya ce, “Muna ganin tasirin talauci a fuskokin mutane da yadda talauci ya zame musu kamar gado. Babban abin da muka sa a gaba shi ne yaki da talauci ta hanyar ajiye bambance-bambancenmu da gina kasa,” kamar yadda sanarwar Daraktan Yada Labarai na Aso Rock, Abiodun Oladunjoye ya fitar.
Ya kuma ce, “Dukkanmu ’yan gida daya ne da muke barci a dakuna daban-daban. Idan muka kalli junanmu a haka muka yi aiki tare, za mu cire mutanenmu daga talauci.”
Shugaba Tinubu ya kuma ce shugabanci na gari ne zai tabbatar da ci gaban Dimokuradiyya a Najeriya.
Kazalika, ya kuma ba Gwamnonin tabbacin cewa kofarsa za ta zama a bude ga dukkan Gwamnonin.