✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole mu dauki matakin kare martabar Al-Qur’ani — Kasashen Musulmi

Jami’ar Al-Azhar ta nemi al’ummar Musulmi da su kai zuciya nesa domin Allah Ya yi alkawarin kare littafinsa.

Kungiyar Kasashen Musulmi ta nemi a dauki matakin kauce wa sake kona Qur’ani, ’yan kwanaki bayan wani ya kona kwafin littafin mai tsarki a Sweden.

Kungiyar mai mamba 57 ta gana a birnin Jeddah na Saudiyya don lalubo martanin da za su mayar kan kona Qur’anin da Salwan Momika, dan asalin Iraki mai shekara 37, ya yi bayan ya tattaka shi a kofar wani masallaci a birnin Stockholm.

’Yan sanda ne suka ba shi kariya kafin ya aiwatar da aniyar tasa, wanda ya ce ya yi hakan ne don ya nuna ’yancinsa na fadar albarkacin baki.

A yau Lahadi, Organization of Islamic Countries (OIC) ta shawarci kasashe mambobinta “su dauki matakin bai-daya don guje wa afkuwar wulakanta Qur’ani,” kamar yadda wata sanarwa da suka fitar bayan taron ta bayyana.

“Dole ne mu ci gaba da tunasar da kasashen duniya game da aiwatar da dokokin kasa da kasa da gaggawa, wadanda suka haramta nuna duk wata kiyayya ga addinai.”

Lamarin ya jawo zanga-zanga a fadin duniya, inda kasashen Musulmi kamar Daular Larabawa da Moroko da Kuwait da Iraki suka kira Jakadan Sweden don nuna bacin ransu.

Allah Zai kare Al-Qur’ani — Al-Azhar

Al-Azhar ta shawarci al’ummar Musulmi da ka da su wuce gona da iri, wajen nuna fushinsu a kan kona Al-Qur’ani da aka yi a harabar babban Masallacin Stockholm.

Shawarar ta Jami’ar Al-Azhar din dai na zuwa ne, a daidai lokacin da al’ummar Musulmin duniya ke ci gaba da nuna fusatarsu da kona al-Qur’anin da aka yi a Sweden.

Kasashe da dama ne dai suka yi tir da yadda aka kona Al-Qur’anin ciki har da Iraki da Iran da Saudiyya da kuma sauran kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Babbar Cibiyar Binciken Addinin Musuluncin ta Duniya ta Al-Azhar din Sheikh Ahmed Mohamed Ahmed El-Tayeb ne dai, ya nemi al’ummar Musulmin duniya da su kai zuciya nesa ka da wautar masu wauta ta sanya su aikata abin da ya saba wa koyarwar addininsu.

Ya kara da cewa babu bukatar yin kone-kone ko kashe-kashe domin an kona Al-Qur’anin, domin ubangiji ya riga ya yi alkawarin kare shi koda azzalumai da miyagu sun ki.