Kungiyar Kafafen Yada Labaran Arewa (NMF) ta bukaci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ta tanadi yanayi da ’yan gudun hijira a yankin za su yi zabe a shekara mai zuwa.
Kungiyar a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a ta hannun Shugabanta, Dan Agbese da Sakatariyarta, Zainab Suleiman Okino, ta ce barin ’yan gudun hijirar su kada kuri’a zai ba su ’yancin amfani da damarsu a matsayinsu na ’yan kasa.
- An zabi ‘yar Najeriya cikin ’yan jaridar duniya da za su samu horo na musamman
- Najeriya Ta Fi Ko’ina Yawan Yara Masu HIV Da Tarin Fuka —WHO
Kungiyar ta jaddada bukatar a zabi dan takarar shugaban kasa da zai iya kawo karshen talauci, sata, ta’addanci, rikicin manoma da makiyaya, Boko Haram da sauran kalubalen da ke addabar Arewa da kasa baki daya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Abin da Arewa ke bukata musamman a wannan lokaci shi ne shiri na musamman da ke da karfin kawo sauyi game da fatara, yunwa da matsalar rashin tsaro; Ba ma son Arewa ta sake shiga cikin mawuyacin hali.
“Muna kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da ’yan gudun hijirar za su kada kuri’unsu da kuma zabar wanda suke so ya mulke su a zabe mai zuwa.
“[Muna bukatar] Duk wanda zai iya kawo karshen ayyukan ’yan bindiga da suka tarwatsa iyalai da yawa.
“Don haka dole mu hada karfi da karfe don kawo wanda zai sauya rayuwar ’yan gudun hijira.
“Arewa ba cibiyar ’yan bindiga ba ce kawai, tana da miliyoyin ’yan gudun hijira gami da hare-haren ’yan ta’adda, rikicin makiyaya da Fulani ya sa jama’a asarar gidajensu da hanyoyin rayuwarsu ta yau da kullum.
“Ya kamata a yi wani abu cikin gaggawa domin mayar da su matsugunansu,” in ji kungiyar.