✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole Hausawa da Fulanin Filato su shiga harkokin siyasa – Nazifi

Tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Malam Muhammad Ahmad Nazifi ya ce dole ne al’ummar Hausawa da Fulanin jihar, su shiga a dama da su…

Tsohon Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Malam Muhammad Ahmad Nazifi ya ce dole ne al’ummar Hausawa da Fulanin jihar, su shiga a dama da su a harkokin siyasa. Malam Muhammad Nazifi ya bayyana haka ne, lokacin da yake jawabi a wajen taron kaddamar da shugabannin Kungiyar Matan Al’ummar Hausawa da Fulani, na kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a garin Jos.

Ya ce wajibi ne al’ummar Hausawa da Fulani a jihar su yi siyasa. Domin addinin Musulunci ya amince a fita a nemi daukaka da nasara  da kasuwanci  da  sauransu.

Ya ce yau a Najeriya  babu yadda za a tafi da kai  a karamar hukuma, ko  a jiha ko a tarayya, dole sai kana yin siyasa.

“Idan muka nade hannu muka koma gefe saboda addini, to muna ji muna ganin addinin zai karye, idan muna gadara da kasuwanci ne muka kame hannu muka zauna, kasuwancin zai iya karyewa. Idan gadararmu zaman lafiya ne muka zaune, zaman lafiyar zai karye. Amma idan muka tashi muka shiga harkar aka yi komai da mu. Aka kawo wanda ake ganin ya dace, sai al’amari ya tafi yadda muke so’,’  inji shi.

Malam Nazifi ya yi bayanin cewa al’ummar Hausawa da Fulani ne  suka taru suka zabi Gwamnan Filato Barista Simon Lalong. “Idan da ba mu zabe shi ba, da watakila ba mu samu abubuwan da muka samu ba.  Don haka ya zama wajibi mu hada kai mu fito mu yi siyasa,” inji shi.

Ya yi kira ga shugabannin kungiyar su ji tsoron Allah, kan wannan jagoranci da aka ba su. Kuma su yi kokari su kwato hakkin matan a  duk inda  aka danne musu.

A jawabin Shugaban Kungiyar Jasawa ta kasa Alhaji Shehu Ibrahim Musalla ya ce al’ummar Hausawa da Fulanin Jos, sun samu dama wajen zabar Gwamnan Jihar Filato da samun shugabancin Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

“Za mu yi amfani da wannan dama idan kuka ba mu hadin kai, don a gyara garin Jos. Kan  illolin da aka yi wa garin, na rashin doka da oda. Na tabbata babu mai farin ciki da sara-suka da ayyukan kungiyoyin asiri da suke faruwa a wannan gari. Don haka muna rokon a ba mu hadin kai, don magance wadannan matsaloli,” inji shi.

Ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar,  su ci gaba da hakuri da junansu, domin a kai ga nasara.

Tun farko a jawabin Shugabar Kungiyar Hajiya Umma Hassan Muhammad ta ce sun kafa  kungiyar ce, domin gwamnati ta san da matan al’ummar Hausawa Fulani na kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa.

Ta ce a da mata ba sa fita su yi siyasa, amma yanzu zamani ya canja suna fitowa ana damawa da su a harkokin siyasa. “Don haka muke son gwamnati ta san da mu, kan duk wasu abubuwan da ake yi a  gwamnati a rika yi da mu,” inji ta.

Taron ya samu halartar manyan ’yan siyasar kananan hukumomin Jos ta Arewa da Bassa da daruruwan matan al’ummar Hausawa da Fulani daga kananan hukumomin.