Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa dole ne dukkan daliban makarantun sakandiren gwamnati da ke fadin Jihar su mallaki Lambar Shaidar Zama Dan Kasa (NIN).
Kwamishinan yada labarai na Jihar, Malam Sanusi Sa’id Kiru wanda ya sanar da hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis.
- Masu kyamar Hip-Hop suna da gaskiya, amma… – Fresh Emir
- Mayakan Boko Haram 50 sun mika wuya a Kamaru
Ya ce umarnin ya hada da daliban matakin ajin karamar sakandire na farko (JSS 1) har zuwa ajin babbar sakandire na karshe (SS 3).
A cewarsa, an bullo da matakin ne domin a sami damar tattara cikakkun bayanan daliban da ke fadin Jihar domin saukaka wa gwamnati wajen tsare-tsare, kasafin kudi da kuma rage magudi lokacin jarrabawa.
Kwamishinan ya kuma ce shirin zai taimaka wa Ma’aikatarsa ta kara samun bayanai ta hanyar daukar zanen yatsu guda goma da kuma karamin hoton fuska da kuma sa hannun kowanne dalibi.
Daga nan sai ya yi kira ga Hukumar da ke Kula da Manyan Makarantun Sakandire ta Jihar (KSSSMB) da ofisoshin ilimi na shiyya-shiyya da shugabannin makantu da daraktoci kan su tabbata an aiwatar da umarnin kamar yadda ya kamata.
Malam Muhammad Kiru ya kuma ce tuni ma’aikatarsa ta kammala shiri da ofishin Hukumar Kula da Shaidar Zama dan Kasa (NIN) da ke Jihar domin saukaka wa daliban mallakar lambar a matakin shiyya-shiyya.