✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole Diezani ta fuskanci shari’a a Birtaniya-Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta dage a kan cewa dole Tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Allison-Madueke ta fuskanci shari’ar zargin cin hanci a kasar Birtaniya Atone-Janar…

Gwamnatin Tarayya ta dage a kan cewa dole Tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Allison-Madueke ta fuskanci shari’ar zargin cin hanci a kasar Birtaniya
Atone-Janar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami shi ne ya yi furucin a ranar Larabar da ta gabata yayin da yake ganawa da manema labaran gidajen rediyon sashen Hausa na kasashen wajen da ke fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar kasa wanda shugaba Buhari ya jagoranta.
Da aka tambaye shi kan shin ko Diezani  za ta iya samun adalci a gida Najeriya sai ya ce “Ai batun ba maganar samun adalci ake yi ba yanzu ana magana ne kan bincike da farko kuma hakan ba ita Misis Diezani Allison-Madueke ce take da ikon fadawa gwamnatin tarayya ta dawo da ita Najeriya don ta bayar da shaida”.