✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Dole Buhari ya tashi tsaye kan Boko Haram’

Dole a wadata jami'an tsaro da kayan aiki na zamani a kuma magance fatara da jahilci

Gwamnonin Arewa maso Gabas sun fada wa Shugaba Buhari cewa dole ya tashi haikan ya magance abubuwan da suka haifar da ayyukan Boko Haram a yankin.

A ganawarsu ta sirri da Shugaban Kasar tare da shugabannin tsaro na kasa, gwamnonin sun jajjada bukatar wadata ’yan sanda da kayan aiki na zamani domin cike gibin da ake da shi a tsaron yankin.

“Mun nuna wa Shugaban kasa muhimmancin Gwamnatin Tarayya ta magance ummul-haba’isin ta’addanci, wadanda suka hada da fatara da yunwa da jahilci da sauransu”, inji gwamnonin.

Shugaban Kungiyar Gwamnnonin Arewa maso Gabas, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya kara da cewa ta haka ne mutanen yankin za su samu damar gudanar da rayuwarsu ba tare da fargaba ba.

Zulum ya ce gabanin ganawarsu da Buhari, Gwamnonin sun tattauna matsalolin yankin da suka hada da rashin tsaro da rashin abubuwan more rayuwa.

Sauran sun hada da batun hakar mai yankin da ma’adanai da kuma farfado da tabkunan ruwa a yankin.

Game da zargin da ake alakantawa da shi bayan harin da kungiyar Boko Hara da kai masa, cewa sojoji sun gaza magance matsalar tsaron Jihar Borno, Gwamnan ya ce: “Ya yi tattaunawa da daya domin ba abin da matsalar Gwamnatin Tarayya kadai ba ce, jihohi da kananan hukumomi su hada kai wajen lalubo mafita ga wannan matsalar a yankin.

“Abun da ya fi muhimmanci shi ne batun tattalin arzikin yankin wanda shi ne babban abun da ya kawo mu. Gwamnati na daukar kwararan matakai domin gaggauta magance wuraren da ake da matsaloli a yankin”

Ministan Tsaro Bashir Magashi da ministan harkokin dan sanda, Muhammad Dingyadi da kuma shugabannin Yan Sanda da na hukumomin tsaro na DSS da NIA duk suna cikin malara taron.

Ya kuma samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbaja da Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa Babagana Monguno da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Ibrahim Gambari.

A bangaren gwamnonin, Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ta Gabas Babagana Zulum na Jihar Borno ya jagoranci takwarorinsa na jihohin Taraba da Gombe da Bauchi da Gombe da Kuma Yobe zuwa tattaunawar.