✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a yi tsayin daka kan rikicin Kudancin Kaduna

Jama'atu Nasril Islam ta ce dole mahukunta su tashi su magance matsalar tun yanzu

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI), ta yi kira ga dukkan wadanda rikicin Kudancin Kadun ya shafa da su yi taka-tsan-tsan yayin daukar matakan da suka dace wajen magance matsalar.

Sakatare Janar na Kungiyar, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce rikicin kabilanci ko na addini yana da wuyar sha’ani wajen magancewa.

A dalilin haka yake kira ga dukkan wadanda abin ya shafa da masu fada a ji, da su tashi wurjajan domin tunkarar lamarin kafin ya wuce gona da iri, yana mai cewa, ‘ice tun yana danye ake tankwara shi’.

Dakta Khalid ya ce kungiyar a karkashin jagorancin Sultan na Sakkwato, Muhammad Sa’ad Abubakar, ta damu matuka kan yadda kashe-kashe da zubar jinin al’umma ta zamto ruwan dare a yankin gami da batutuwa marasa dadi da ake yi dangane da lamarin.

Ya ce Sarkin Musulmi yana takaicin munanan furuci ke fitowa daga bakunan al’umma ciki har da dattawan kasar wadanda a cewarsa “sun cancanci yin amfani da kafofin sadarwa wajen kwantar da hankalin mutane amma sun buge da tunzura lamarin wanda ka iya tayar da husuma a cikin al’umma”.

Da wannan ne Sarkin Musulmi ya ke kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna ta kara kaimi wajen kawo karshen barazanar da ta addabi al’umma a Kudancin Kaduna wadda ta shafi kasar baki daya.

“Dole Gwamnati ta yi dukkanin mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan musiba wajen sauya ta da aminci .”

“Kuma kada mu kuskura mu yi kasa a gwiwa wajen rokon Allah Ya kawo mana sauki.