Tsohon Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Tsaron Cikin Gida, Hon. Aminu Sani Jaji, ya shawarci Majalisa da bangaren zartarwa su su samar da asusu na musamman domin shawo kan matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.
Hon. Jaji, ya ce kasafin da ake ware wa bangaren tsaro a Najeriya sun yi kadan, don haka, bangarorin su fadada tunaninsu su kafa kwamiti na musamman domin sayen makamai da samar da kayan tsaro na zamani domin kawar da matsalar miyagun laifuka a kasar.
- An kai hari a rugar Fulani a Abuja
- ’Yan Najeriya na cikin firgici, babu wanda ya tsira a Najeriya —Dahiru Bauchi
- Ya halasta mai azumi ya sha abun kara kuzari —Sheik Lawan Abubakar
- ’Yan bindiga sun saki sabon bidiyon daliban Kwalejin Afaka
“Majalisar Tarayya na da muhimmiyar rawar takawa wajen magance matsalar. Idan ka lura, za ka ga kasafin bangaren tsaro ya yi kadan ya iya magance matsalar, don haka ya kamata ta yi wani abu,” inji shi.
Ya shaida wa ’yan jarida cewa, “Lokacin da nake Shugaban Kwamitin Tsaron Cikin Gida a Majalisa, akwai lokacin da aka yi kasafi, amma hukumomin tsaro kashi 60 na kasafin aka ba su.
“Ko kashi 100% aka ba su ya yi kadan, ballantana kashi 60%, saboda haka dole Majalisa ta yi wa al’amarin kallo na tsanaki.
“Akwai dabarun da ya kamata bangarorin biyu su samar a bangaren tsaro ta yadda haka za ta cimma ruwa, a cikin wata uku zuwa shida.
“Su hadu su kafa asusu na musamman. Bangaren zartarwa ya kafa kwamitin yin sayyaya wanda zai kunshi duk bangarorin da suka dace, tare da samar da duk abubuwan da bangaren tsaro ke bukata.
“Bangarorin su hada kai su samar da kayan aiki don murkushe barazanar tsaro. Amma dai a halin yanzu sai dai mu yi ta addu’a,” inji shi.