✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dole a shiga Sambisa kafin a gama da Boko Haram —Zulum

Har yanzu ina kan bakata cewa sojoji na yin zagon kasa a yaki da Boko Haram, inji shi

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi zargin kungiyar Boko Haram da ci gaba daukar mutane su taya su yaki, ciki har da wadanda suka tilasta wa zama ‘yan gudun hijira.

Gwamnan ya alakanta hakan da rashin samun abin da jama’ar ke bukata a sansanonin gudun hijrar, musamman damar komawa garuruwansu domin su ci gaba da noma da sauran sana’o’in da su ka saba.

“Gaskiya ne kungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga cikinta kuma hakan kuma abin tsaro ne”, inji gwamnan.

A hirarsa da Sashen Hausa na BBC, ya kara da cewa: “Mutane sun gaji da zama a sansanin masu hijra. Ba su samun abin da suke so.

“Dole ne su koma garuruwansu domin samun damar yin noma da kiwo kasancewar babu wata gwamnati da za ta iya samar da ciyarwa gare su mai dorewa”.

Gwamnan wanda ya ce sun samu nasarar mayar da mutane garuruwan Kukawa da Mafa sannan nan gaba “za mu mayar da mutanen Kawuri.”

“Amma muna fatan sojoji za su kara kaimi wajen ganin an mayar da al’ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala,” inji Zulum.

— Dole sai an je Sambisa an gama da Boko Haram

Kazalika, gwamnan ya ce yanayin tsaro ya dan inganta a jihar tasa sabanin shekarun baya, ko da yake ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba domin Boko Haram na maboyarsu.

“Yan kungiyar na fakewa a tabkin Chadi da kuma dajin Sambisa. Kuma idan har ba a bi su har ciki ba an kore su to fa akwai matsala. Korar su daga hedikwatarsu ita ce hanya guda daya ta kawo karshen Boko Haram”, inji gwaman.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wani yanki na jihar da yanzu haka yake karkashin ikon kungiyar ta Boko Haram.

Amma har yanzu yana nan a ka bakarsa cewa sojoji na yi wa kokarin yaki da ‘yan ta’addan zagon kasa.

“Da farko har yanzu ban janye kalamaina ba. Ina kan bakata kan cewa ana yi min zagon kasa.

“Amma dai ban kama suna ba. Ban ce Shugaba Buhari ba. Saboda duk wani abu da za a yi ya haifar da cikas ga yaki da Boko Haram zagon kasa ne.

“Idan aka bayar da kudin makamai sai sojoji suka ki siya ka ga wannan ai zagon kasa ne. Kai hatta rashawar nan da ake fama da ita, ita ma ai zagon kasa ce.”

— A kan cire hafsoshin tsaron kasa

A kan kiraye-kirayen da ‘yan Najeriya ke yi ga Shugaba Buhari ya kori manyan hafsoshin tsaron kasa kuwa, Zulum ya ce, “Cire manyan hafsoshin tsaro ba abin da ya dame ni ba.

“Burina shi ne a samar da zaman lafiya a jihar Borno.

Tsarin mulkin Najeriya ya fayyace hanyoyin da shugaba zai bi domin yin nadi ko kuma sauyin hafsoshin tsaron kasa.

“Ni wannan ba abun da ya shafe ni ba ne. Shugaban Kasa ne ke da wuka da nama”.