Sanata Ali Ndume ya bukaci Shugaba Buhari ya kayyade wa sabbin Manyan Hafsoshin Tsaro wa’adin kawo karshen ta’addanci a Najeriya kuma ya gaggauta korar su in suka gaza.
A tsokacinsa kan nadin Manyan Hafsoshin Tsaron, Ndume wanda shi ne Shugaban Kwamitin Sojin Kasa na Majalisar Dattawa, ya bukaci Shugaban Kasar ya ba su duk abin da suke bukata domin cimma nasara.
- Kotu ta kwace kudaden tsohon Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari
- Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100
- Abu 5 da ke sa masoya batawa a lokacin hira
- ’Yan bindiga sun kai hari mahaifar Shugaban Majalisar Zamfara
“Ina goyon baya, musamman yanzu da aka nada sabbi Hafsoshin Tsaro, cewa a ba su kudaden da suke bukata na aiwatar da yakin a lokaci guda, a cire su daga jerin hukumomi masu karbar kudade bayan duk wata uku.
“Daga nan sai Shugaban Kasa ya zauna da su ya ba su wa’adi, ya ce ‘kun bukaci kaza da kaza kuma na ba ku, yanzu ba sauran abun da ya rage. Saboda haka ku fada min lokacin da za ku kammala wannan yakin.’
“Abin da ya kamata ya yi alkalancin a kan wa’adinsu ke nan; idan sun kasa kar gwamnati ta bata lokaci wajen tisa keyarsu,” inji shi.
Sai dai ya ce sabbin shugabannin sojin da aka nada suna da kwarewar da ta dace na sauke nauyin da aka nada musu.
A cewar Sanata Ndume, sauye-sauyen na Buhari sun nuna cewa shi mai fada da cikawa ne a kan alkawarin da ya yi na sauya fasalin tsaron Najeriya.
“Wannan na cikin sauye-sauyen da ya yi alkawari; kuma mutanen da ya nada suna da kwarewa da cancantar da ta dace,” a cewarsa.
Ndume ya ce ya kamata Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa, kuma ya jagoranci ayyukan shugabannin tsaron.
Sannan kuma ba laifi ba ne su bi ta Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, domin akwai bukatar samun fahimtar juna da hadin kai a tsakaninsu.
“Ya kamata a kafa dakin tara bayanai da kuma tabbatar da tattara bayanan sirri tare da amfani da su,” inji shi.
Abdullateef Salau da Sagir Kano Saleh