Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ya yi Allah-wadai da yawaitar safarar kananan yara da ake sacewa daga yankin Arewa zuwa Kudancin Najeriya.
Sarkin ya bayyana damuwarsa yayin zantawarsa da manema labarai ranar Asabar, ya kuma ce dole a gaggauta magance matsalar.
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Kauce Wa Talauci A Watan Janairu
- Muna Neman Fansan Jinin Ammi Mamman —’Yar gwagwarmaya
A ranar 27 ga watan Disambar 2023 ne rundunar ’yan sandan jihar ta bankado wani wajen yin garkuwa tare da safarar kananan yara.
Rundunr ta kuma ce akalla mutum 9 da ke yi wa baragurbin aiki a jihohin Kano, Bauchi, Legas, Delta, Anambra da kuma Imo suka shiga hannu.
Rundunar ta sanar da cewar akalla kananan yara bakwai daga cikin wadanda aka ceto akasarinsu ’yan asalin Jihar Bauchi ne.
Shi ma Shugaban kabilu da ke a Kano, Boniface Igbekwe, ya yi tir da tsanantar matsalar tare da yin kira ga hukumomi su yi duk mai yiwuwa wajen kama masu hannu a ciki don kawo karshen matsalar.