Sahabi Aliyu (RA) ya fadi ga Jabir dan Abdullahi (RA) cewa “Duniya ta dogara ne a kan abu hudu; addini da malami mai yin aiki da iliminsa, sai jahili wanda ba ya girman kai wajen neman sani da kuma mawadaci wanda ba ya rowa da dukiyarsa.”
Marigayi Sheikh Dokta Ahmad Muhammad Ibrahim wanda aka fi sani da Dokta Bamba ya ce ilimi ba komai ba ne sai sanin abu a zuciya da kuma gaskata shi a zahiri, yayin da jahilci ke nuni da kiyaye abu a zuciya wanda a zahirance ba gaskiya ba ne.
- Na yi ‘nadamar rera “Yau Najeriya riko sai mai gaskiya” – Mawakin Buhari
- Dalibi ya bindige abokinsa a cikin aji
Saboda haka, a cewarsa ba kawai rashin sanin abu ake kira jahilci ba, a’a har ma da sani gami da riko da abin da bai gaskata ba.
Rayuwa irin ta Dokta Ahmad madubi ce ga daukacin al’ummar Musulmi.
Mutum ne mai kyakkyawar fahimta ga lamurran addini, amma mai zafafawa wajen kare martabar Annabi Muhammad (SAW).
Mai kimanin shekara 82 a duniya, wanda ya rasu a ranar Juma’a, 7/1/2022, marigayi Dokta Ahmad Bamba ya shafe daukacin rayuwarsa wajen nema da kuma yada ilimi.
Ya shafe sama da shekara 20 yana daukar darasi a Masallacin Annabi Muhammad (SAW) a Madina.
Sannan ya fassara Littafin Muwadda na Imamuna Maliku ɗan Anas daga harshen Larabci zuwa harshen Hausa, baya ga karantar da manyan littattafan Hadisi irin su Sahih Bukhari da Sahih Muslim da Sunanu Abu Dawud da Sunanu Nisa’iy da Sunanu Tirmizi da Sunanu Ibn Maja da Sunanu Darimi da Musnad Ahmad bn Hambal da sauransu duk a cikin harshen Hausa.
Tabbas, rasuwarsa babbar asara ce ga kafatanin al’ummar Musulmi musamman Hausawa.
Ya zo a cikin littafin ‘Al ilmu Huwal Imamu’ na Sheikh Ibrahim Nyassi cewa hanyar Aljanna tana hannun mutum hudu: Malami da mai gudun duniya da mai ibada da kuma mai jihadi fi sabilillahi.
Shi malami idan ya kasance mai gaskiya ne a cikin zuciyarsa, tabbas Allah zai azurta shi da hikima.
Duk kuwa wanda aka bai wa hikima alal hakika an ba shi gagarumar baiwa a nan duniya da gobe Lahira kamar yadda yadda ya zo a cikin Littafin Allah wato Alkur’ani.
An tambayi Dan Mubarak cewa su wane ne mutane? Sai ya ce ‘Malamai,’ sai aka ce masa su wane ne sarakuna? Sai ya ce ‘masu gudun duniya,’ sai aka ce su wane ne kaskantattu? Sai ya ce ‘masu cin duniya da addini.’
Don haka, ana iya cewa lallai malamai mutane ne masu daraja a cikin al’umma.
Abdul’aswad yana cewa babu wani abu wanda ya fi ilimi daukaka. Sarakuna masu yin hukunci ne ga jama’a, yayin da malamai ke yin hukunci a gare su.
Ahnaf (RA) yana cewa malamai sun kusa kasancewa iyayen giji, dukkan daukakar da ba a karfafe ta da ilimi ba, karshen ta kaskanci ne.
Annabi Muhammad (SAW) ya ce “Malamai su ne magada Annabawa.” (Tirmizi, Abu Dawood da Ibn Maja duk sun ruwaito shi) Allah Ta’ala kuwa Ya ce, “Iyaka dai masu jin tsoron Allah su ne malamai.” (Suratul Fathi, 28).
Babu bukatar zurfafa yabo ga marigayi Malam Ahmad Bamba, domin shi ba mai son yabo ko kwarzantawa ba ne a zamanin rayuwarsa, amma yana gaba-gaba wajen jaddada Sunnah a Kasar Hausa bayan da ta dauko dusashewa.
Mutum ne shi wanda yake son Allah da ManzonSa (SAW), wanda yake tarbiyyantar zukatan bayin Allah a kan bautar Allah ta tsanin ManzonSa Annabi Muhammad (SAW) da mayar da lamura ga AlSadiq Tukur Gwarzolah, kuma mutum ne marar kwadayi, mai darajanta ilimi da darajanta kansa, gami da fadar gaskiya walau ga shugabanni ko ga mabiyansu.
Allahu Akbar! Shi mutum ne mai daraja a duniyar Musulunci, tushen darajarsa kuwa bai wuce ga rikonsa ga Sunnar Annabi Muhammad (SAW) ba da tsantseninsa, kai ka ce shi ne Imam Maliku bn Anas ko Imam Hasanul Basri.
Hakika rayuwarsa ta kasance abar koyi ga al’ummar Musulmi.
Wani sashen masana sun ce an fifita Imam Hasanul Basri a kan sauran Tabi’ai ne saboda abubuwa biyar:
1. Ba ya umarni da aikata wani aiki face ya fara aikatawa.
2. Ba ya hana wani aiki face ya fara hanuwa daga gare shi.
3. Duk wanda ya nemi wani abu daga abin da Allah Ya hore masa zai ba shi.
4. Ya kasance yana wadatuwa da iliminsa ga barin neman wani abu a wajen mutane.
5. Ya kasance ciki da wajensa duk daya ne.
Tabbas duk wadannan siffofi biyar sun tabbata ga marigayi Sheikh Ahmad Ibrahim Bamba.
Ga shi kuma ya samu cikawa irin tasa, da fatan Allah Ya rahamshe su duka amin.
Abdullah bin Amr Ibnul Ass ya ruwaito daga Annabi Muhammad (SAW), cewa “Lallai, Allah ba Ya dauke ilimi daga hana shi ga bayinSa.
Sai dai Yana dauke ilimi ne daga mutuwar malamai ta yadda tsarkakakkun mutane za su gushe, sai mutane su nada wawayen (jahilai) mutane a shugabanci (su dauke su malamai).
Sannan idan aka tambaye su, sai su yi magana ba da ilimi ba. Sai su taɓe kuma su yi asara.” (Bukhari da Muslim suka ruwaito).
Muna juyayin rashin babban masani Dokta Ahmad Bamba, to amma ya kamata kowa ya sani wannan duniya ba abar dawwama ba ce.
Kowane mai rai zai dandana mutuwa. Kuma tabbas, yadda Dokta Ahmad ya koma ga Mahaliccinsa, kowanenmu lokaci yake jira domin komawa ga Allah.
Don haka, ya kamata mu shagaltu wajen aiki da koyarwarsa da neman ilimi da bin Allah da kuma neman dacewar Allah da samun Aljanna.
Allah Ya gafarta wa Dokta Ahmad Ibrahim Bamba, Allah Ya tallafi bayansa, amin.