Wani ma’akacin kamfanin wutar lantarki na Ibadan, IBEDC, ya sha dan karen duka a hannun wasu da suka fusata bayan ya raba masu takardun biyan kudin wuta.
Lamarin dai ya faru ne ranar Alhamis bayan da jami’in mai suna Ayorinde Olajide ya shiga unguwar Isale Igbeyin da zummar rarraba wa mazauna unguwar takardun biyan kudin wutar lantarki inda wasu da suka fusata suka hau shi da duka.
Ayorinde ya ce yana tsaka da raba takardun a yankin Isale Igbeyin sai wasu mutane suka far masa,
“Ban ankara ba sai na ji sun rufe ni da duka suna cewa na daina raba takardun kudin wutar lantarkin; kafin na ce uffan sun lakada min dukan kawo wuka har sai da maigidana ya zo da mota da zummar ya cece ni amma wani daga cikinsu ya biyo ni cikin motar ya dake ni a ido, ya yi min mummunan rauni”, inji shi.
Mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma shaida wa Aminiya cewa ‘yan sandan jihar da ke aiki a ofishin hukumar na Ibara sun kama mutum biyu da ake zargi da dukan jami’in kana ana bincikar su, yayin da aka garzaya da jami’in asibiti domin kula da lafiyarsa.