Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abun a yaba kan kin sanya hannu a kan sabuwar dokar zabe da Majalisar Dokokin kasar ta amince da ita.
Shugaban kungiyar kuma Gwamnan Jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya bayyana hakan bayan wata ganawa da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja a ranar Talata.
- Soumana Boura: Faransa ta kashe jagoran kungiyar IS na Nijar
- Aisha Buhari ta bai wa ma’aikatanta hutu har sai ta neme su
Ya ce gwamnoni ba sa adawa da duk wani shiri na fitar da ’yan takara, sai dai ya kamata a yi abun da hankali zai dauka.
Gwamnan ya ce “Bajintar da shugaban kasa ya yi ta amincewa da ra’ayin jama’a abun a yaba masa ne, domin abun da shi yake so shine a yi wa kowa adalci ko ma wane tsari za a bi.”
Su dai ’yan Majalisar Dokokin Najeriya sun kafe a kan cewa amincewa da sabuwar dokar ne kadai maslaha, wajen shawo kan irin karfa-karfar da gwamnonin ke yi wajen gudanar da zabukan cikin gida na jam’iyyu.
Dalilin da na ki amincewa da Dokar Zabe —Buhari
Shugaba Buhari ya bayyana dalilan da suka sa hana shi sanya hannu a kan sabuwar dokar zaben kasar da majalisa ta amince da ita tun a watan jiya.
Cikin wata wasika da Buhari ya aike wa Majalisar Dattawan Najeriya, ya ce daga cikin da suka hana shi sanya hannu a sabuwar dokar akwai matsalar tsaro da kuma tsadar gudanar da tarurrukan jam’iyyun siyasa.
Shugaban ya bayyana haka ne a wasikar da ya rubuta wa shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawal bayan cikar wa’adin kwanaki 30 da gabatar masa da dokar.
Sauran dalilan da Buhari ya wassafa sun nuna cewa halin da ake ciki yanzu a kasar ba zai bashi damar sanya hannu a kan dokar ba saboda tsadar gudanar da zaben fidda gwani na ’yar tinke da ake kira kato-bayan-kato da take hakkin jama’a da kuma hana kananan jam’iyyu ’yancin da suke da ita.
A cewarsa, ya samu gamsassun shawarwari daga ma’aikatun gwamnatin da kuma wasu hukumomin kasar wadanda ya yi nazari a kansu kafin yanke hukuncin kin sanya hannu a dokar zaben la’akari da halin da kasar take ciki a yau.
A kan haka ne Buhari ya ce abin da yafi dacewa shi ne a bai wa kowacce jam’iyya dama ta zabarwa kanta abinda take so wajen tsayar da ’yan takararta.
Ana iya tuna cewa, a ranar 19 ga watan Nuwamba ne Majalisar dokoki ta mika wa Shugaba Buhari sabuwar dokar zaben wadda ta kwashe kwanaki 30 ba tare da rattaba hannu a kai ba.
Sai dai wannan mataki da Shugaba Buhari ya dauka ya gamu da cikas daga sassa daban daban na kasar sakamakon fatar da ake yi na ganin sabuwar dokar ta kakkabe hannun gwamnonin jihohin kasar dangane da yadda suka yi wa jam’iyyun siyasar dabai-bayi wajen tsayar da wadanda suke son takara da kuma hana wasu tsayawa.
Yanzu haka wasu ’yan Majalisar Tarayya na barazanar yin amfani da karfin mulkin da kundin tsarin mulkin ya basu wajen amincewa da dokar ba tare da goyan bayan shugaban kasar ba.
A karkashin kundin tsarin mulki, Majalisar Dokokin Tarayya na iya amincewa da doka idan ta samu kuri’u kashi biyu bisa uku na yawan ’yan majalisun tarayya da suka goyi bayan dokar.